1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Waye Dr. Mahathir bin Mohammad

Bashir, AbbaJuly 8, 2008

Taƙaitaccen tarihin Dr. Mahathir bin Mohammad, tsohon Fira ministan Males

https://p.dw.com/p/EYjW
Mahathir bin MohammadHoto: AP

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Barr. Ɗanlami Alhaji Wushishi na ma'aikatar shari'a dake Minna a jihar Naija ta tarayyar Najeria. Ya ce; Don Allah ku ba ni tarihin Dr. Mahathir bin Mohammad, tsohon Prime Ministan Malesiya.

Amsa: An haifi Dr. Mahathir bin Mohammad ne a ranar 20 ga watan disamba,1925 a wani gari mai suna Alor Star, babban birnin jihar Kedar, da ke arewacin jihar. Mahaifinsa malamin makaranta ne ɗan asalin ƙasar Indiya, daga jihar Kerala inda yai hijira, sannan mahaifiyarsa ‘yar Malesiya ce, amma Dr. Mahathir ya fi danganta kansa da dangin mahaifiyar tasa.

Shi dai Dr. Mahathir ɗan siyasa ne, kuma ya fara harkar siyasa ne tun shekara ta 1945, in da ya fara harkar ƙungiya a cikin wata ƙungiya mai suna Anti-Malayan Union Campaign. Sannan ya shiga wata ƙungiyar siyasa mai suna United Malays National Organisation, a lokacin da aka kafa ta a shekara ta 1946. A matsayin sa na shugaban jam'iyyar kuma shugaban kwamitin siyasar, ya yi baƙin jini sosai a lokacin da ya ba da shawarar cewa, ya kamata a riƙa bin wasu ƙa'idoji kafin a zaɓi ‘yan takara don zaɓen shekatar 1959.

Dr.Mahathir bin Mohammad ya zama Prime Minista a ranar 16 ga watan yuli, shekara ta 1981, bayan Prime Minista mai ci a lokacin wato Hussain Onn, ya yi murabus bisa dalilan rashin lafiya. A lokacin, Dr. Mahathir shi ne ya zama Prime Minista na huɗu na ƙasar Malesiya, sannan ya fito ne daga ƙaramin gida, a yayin da sauran ukun da suka yi kafin sa, sun fito ne daga gidan sarauta. Hasali ma dai bayanai sun tabbatar da cewa, a lokacin da yake matashi, ya taɓa yin tallar kayan abinci a ƙoƙarinsa na ɗaukar nauyin iyayensa. To ya dai riƙe wannan miƙami na Piraminista har tsawon shekaru 22, wato daga 1981 zuwa shekara ta 2003; wanda kuma ya sa shi ya fi kowanne Prime minister daɗewa a karagar mulki a ƙasar Malesiya, kuma shugaba mafi daɗewa a shugabanci a nahiyar Asia.

A lokacin da yake karagar mulki, tsare-tsaren da ya ɓullo da su na tafiyar da gwamnati bisa kishin ƙasa, ya sa ƙasar malesiya ta bunƙasa ta hanyar ƙere-ƙere, kasuwanci da hanyoyin sadarwa.

Bayan shekaru 22 a kan kujerar mulki, Dr. Mahathir ya yi murabus a ranar 30 ga watan oktoba na shekara ta 2003 kuma an ba shi lambar yabon da ta fi kowacce a ƙasar Malaysia.

Sannan bayan Dr.Mahathir ya yi murabus, sai kuma ya sanar da janyewar sa daga cikin jam'iyyar UMNO a ranar 19 ga watan mayun wannan shekara ta 2008, sannan ya buƙaci sauran mambobin jam'iyyar da su ma su janye, da nufin tilasta wa shugaban jam'iyyar mai ci, wato Abdullah ya sauka. Amma bai yarda ya shiga wata jam'iyya ba, kuma ya ce zai koma jam'iyyar ta UMNO ce kawai idan Abdullah ya sauka.

Dr. Mahathir ya yi suna a ƙasashen yammacin duniya saboda sukar da yake yawan yi, na al'amuran ƙasashen yammacin duniya, musamman ma dai ƙasar Amurka.