1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Waye ya kirkiro wasan wuta

Abba BashirAugust 28, 2006

Bayani game da asalin wasan wuta

https://p.dw.com/p/BvVI
wasan wuta
wasan wutaHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun,malam Aliyu Iliyasu, Gwagwalada, Abuja, Najeriya. Ya ce; Waye ya kirkiro wasan wuta irin na zamani wanda ake kira da suna (Fireworks) a Turance,kuma meyasa ake danganta shi da ranar 4 ga watan yuli?

Amsa: To wasan wuta dai irin na zamani, wasane da ya samo asali , tun zamanin wata dadaddiyar daula a kasar Sin , wato Chaina, wadda ake kira da suna Daular Han, wato daula ce da ta kafu tun shekaru (206 BC-220 AD). Saboda haka abu ne mawuyaci,a iya cewa ga mutumin da ya gano ko kuma ya kirkiro wannan wasa. Amma dai zamu iya yin bayani a game da dalilin da yasa ake danganta wannan wasa da ranakun samun yancin kann kasa.

Ranar 4 ga watan Yuli, 1777, ita ce rana ta farko da aka yi bikin samun yancin wata kasa a Duniya. Wannan kasa kuwa ita ce Amurka. Kuma hakan ya faru ne shekara daya, bayan da kasar ta Amurka ta samu yancin mulkin kanta da Turawan mulkin mallaka na Ingila.To a farkon shekarun 1800, sai aka shigar da al’adu irin na fareti da bukukuwa, aka kuma tabbatar da wasan wuta irin na zamani a matsayin wata alama ta bukin murnar ranar yancin Amurka. Saboda haka tun daga wannan lokaci ake amfani da wasan wuta, bawai ranar samun yancin kan Amurka kawai ba , a’a harma da ranar samun yancin kan sauran Kasashe a Duniya.

Kamar yadda wani sashe mai bayani game da kagaggun abubuwa a cikin na’ura mai kwakwalwa, wato (Inventhelp) a Turance ya tabbatar. Ya nunar da cewa, wasannin wuta na farko da akai da can, wasu sanduna ne na gora ake cinna musu wuta. Kuma mai makon yin amfani da su wajen bukukuwa, sai ake amfani da su wajen gargadi, saboda wannan tsananin karar na tartsatsin wuta da suke bayarwa. Masu wannan wasan wuta sun yi Imanin cewa, ya na kau da sharrin shaidan musamman ma idan wani hadari ya tunkari mutane.Amma shi wasan wuta irin na zamani, wasa ne da ya watsu cikin Duniya bayan da Mutan Kasar Sin wato Chaina, suka kirkiro da bindigar toka, shekaru da yawa da suka wuce.