1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Waye ya kirkiro Wayar-salula

Abba BashirAugust 6, 2007

Bayanin mutumin da ya kirkiro wayar Salulu

https://p.dw.com/p/BvUl
Wayar-Salula Kirar Motorola
Wayar-Salula Kirar MotorolaHoto: DW

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Tambaya ta farko a shirin namu ta fito daga hannun Abdulmalik Muhammad daga Jamhuriyar Niger, Malamin cewa ya yi , Don Allah ina so ku sanar da ni Mutumin da ya kirkiro wayar Salula a Duniya,Dan wace kasa ne, kuma wane irin karatu ya yi. Kuma idan da hali ku sanar da ni ranar da ya kirkiro wannan waya, da kuma mutumin da ya fara buga wayar salula da kuma wanda aka fara kira?

Amsa: Babu shakka batun wayar salula abune da ya dabaibaye Duniya a Halin yanzu. Da dai kafin zuwan wayar Salula, Mutane suna rayuwarsu ne hankalinsu a kwance, amma yanzu da wayar Salula ta zama ruwan-dare game Duniya, babu wanda yake so ya rayu ba tare da ita ba. To shin zargi zamu yi ko kuma godiya ga wanda ya kirkiro mana da wanna abu , wanda yake cinye wa mutane kudi? To imma dai zarginne ko kuma yabon, to wanda za’a zarga ko kuma a yaba shine Dr. Martin Cooper.

Shi dai Dr. Cooper Dan kasar Amurka ne, kuma an haife shi ranar 26 ga Disamba, 1928. Ya girma a garin cikago kuma ya yi digiri a fannin Injiniyan lantarki. A shekarar 1954 ne, kamfanin Motorola ya dauki hayar sa, inda ya yiwa kamfanin aiki wajen samar da yan-madaidaitan kayayyaki, musamman ma dai na sadarwa. Daga cikin abubuwan da ya yi wa wannan kamfani har da radiyon hannu ta sadarwa tsakanin yan-sanda. Kai shine ma mutumin da ya fara yin irin wannan radio ta sadarwa a Duniya, a shekara 1967. Daga nan ne ya zama shugaban bincike na wayar salula a kamfanin na Motorola.

To Dr. Martin Cooper ya samar da wayar Salula a 1973, lokacin da yake aiki da kamfanin Motorola, a hakika shine Mutumin da ya samu nasarar yin kira na farko a Duniya ta amfani da wayar Salula. Kuma ya yi wannan kira ne daga wani wajen hada-hadar Mutane a garin New York, Ranar 3, ga watan Afrilu, 1973. In da ya kira wani abokin hamayyarsa yace da shi“Joe ina kiranka ne da wata na’urar wayar Salula ta hannu yar-madaidaiciya’’

Bayan shekaru 10 da kirkiro ta ne, aka fara sayar da wayar ta Salula a kasuwa, lokacin da kamfanin Motorola ya fara fito da ita akan farashi na $3,500. Amma abin mamaki duk da wadannan makudan kudi na wayar ta Salula a wancan lokaci, amma ba tare da wani tsawon lokaci ba, sai wannan sabuwar fasaha ta samu karbuwa ka’in da na’in.