1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Weah zai kwaskware kundin tsarin mulkin Laberiya

Gazali Abdou Tasawa
January 30, 2018

Sabon shugaban kasar Laberiya George Weah ya bayyana aniyar yi wa kundin tsarin mulkin kasarsa gyaran fuska domin cire wasu matakai da ya tanada da ba su dace da tafiyar zamani ba.

https://p.dw.com/p/2rkZL
Liberia Wahlen George Weah
Hoto: picture alliance/dpa/epa/A. Jallanzo

Kundin tsarin mulkin ya tanadi haramta wa wadanda ba bakar fata ba takardar iznin zaman dan kasa a kasar ta Laberiya. 

Shugaba Weah ya  bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da ya gabatar a gaban 'yan majalissun kasar a jiya Litinin  inda kuma ya soki lamirin matakin da ke haramta wa 'yan asalin kasashen waje mallakar filin noma, matakin da ya ce na taimakawa ga hana masu niyyar saka jari na ketare zuwa cikin kasar.

 Kazalika shugaban na Laberiya ya soki lamrin matakin da ke haramta wa 'yan kasar ta laberiya izinin mallakar takardar izinin zaman dan kasa a wata kasar ta daban, matakin da ya ce bai dace ba ta la'akari da yadda 'yan aksar ta laberiya da dama da suka bar kasar a loakcin yakin basasa na shekarun 1989 zuwa 2003 sun fake a wasu kasashen inda aka kuma ba su takardar izinin zaman 'yan kasa.

 

Bugu da kari Shugaba Weah  ya sanar da cewa zai rage kudin albashi da na wasu alawus nasa da kashi 25 daga cikin dari kana  ya yi kira ga 'yan majalissun kasar suma su yi haka.