1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WEen Jiabao ya kammala rangadin kasashen Afirka

June 24, 2006
https://p.dw.com/p/Buse
Firaministan China Wen Jiabao ya kammala rangadin kasashe 7 da ya kai a Afirka da nufin karfafa huldodi tare da samarwa kasarsa danyun kaya don bunkasa tattalain arzikinta. FM Wen ya tashi daga Uganda bayan tattaunawa da shugaba Yoweri Museveni inda bangarorin biyu suka sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama da suka hada da na hadin kan tattalin arziki, fasaha, samar da makamashi da dai sauransu. Ziyarar ta Wen ita ce ta 3 da manyan jami´an China suka kaiwa nahiyar Afirka a wannan shekara. Masu sukar lamirinta na zargin gwamnatin Beijing da kwadayin albarkatun da Allah Ya huwacewa Afirka ba tare da ba da fifiko ga keta hakkin bil Adama ba. Rangadin FM ya kai shi kasashen Masar, Ghana, Janhuriyar Congo, Angola, Tanzania da kuma ATK.