1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar Yaƙi da cutar HIV/AIDS

Zainab MohammedDecember 1, 2008
https://p.dw.com/p/G6gS
Hoto: AP

Yau ce ranar da Majalisar Ɗunkin Duniya ta keɓe domin yaki da cutar AIDs mai karya garkuwar jiki.Inda masu shirya gamgamin wannan rana ke cigaba da jaddada bukatar samarda kulawa da magunguna ga waɗanda suka kamu,tare da kuma kariya ga Al'umma.


Majalisar Ɗunkin Duniya tayi nuni dacewar matsalolin tattalin arziki da duniya ke fama dashi a halin yanzu yana iya haifar da babbar illa wa yaki da cutar HIV/AIDS,idan har kasashe dake bada tallafin yaki da cutar sun janye hannayensu.

Babban jami'in hukumar UNAIDS dake kula da cutar Paul De Lay,yayi nuni dacewar matsalar tattalin arzikin zai shafi dukkan shirye-shirye shirye na tallafi da ake bayarwa.

A taron manema labaru daya gudanar yau domin bukin wannan rana,De Lay ya jaddada cewar dole ne kasashe masu cigaban masana'antu su cigaba da dukkan tallafi da suke bayarwa kasashe matalauta da masu tasowa.

Yace nan da shekaru 4- 5 masu gabatowa,za a iya fuskantar matsaloli wajen samarda magunguna na yaki da kwayoyin HIV idan har aka samu tsaiko na tallafi a yanzu.


Akwai kimanin mutane million 33 dake rayuwa da kwayoyin Hiv mai haifar da cutar Aids bisa ga  kididdigan karshen shekatara ta 2007.A yayinda Kasashen nahiyar Afrika dake yankin kudu da Sahara.Botswana dai na daya daga cikin kasashen Afrika da Cutar Aids tayiwa katutu,inda magabatan kasar a ahalin yanzu suka mike tsaye wajen shawon yaduwarta da kulawa da wadanda suka kamu inji tsohon shugaban Botswana Festus Mogae.....


" A yanzu muna mayar da hankali ne akan kariya.Mun gano cewar sauyin yanayi na rayuwa yana da muhimmanci,muna ganin yadda mutane  ke cigaba da mu'amala ,da kuma shaye-shaye,wadamda sune ummul aba'isin  habaka yaduwarsa.Duk dacewa ana samun koma baya  tsakanin matasa.Yanzu zamu kaddamar da yaki ne akan sauyin yanayi na rayuwa daura da dukkan wasu matakai da muke dauka"


Bostwana dai na mai zama daya daga cikin kasashen dake yankin kudancin afrika da AIDs tayiwa katutu.Festus Mogae wanda ya shugabanci kasar daga shekarata 1998 zuwa 2008,ya taka muhimmiyar rawa wajen yaki da cutar,duk dacewar yace akwai matsaloli dake tattare da hakan...


"Akwai matsalar saɓanin ra'ayi a mulki irin na Demokraɗiyya .Munso da ace duk mutuminda yaje asibiti domin kowane irin rashin lafiya a ,ayi masa gwajin Aids ako da yaushe,amma dokokin kare hakkin bil'adama ,basu amince da hakan ba.Adangane da haka ne sai wanaya ya yarda ake masa gwajin"


A yanzu haka dai akwai shirye shirye masu yawa da gwamnatoci suka kirkiro na wayerwa da jama'a kai dangane da illolin wannan cuta,kuma bisa ga rahotan Majalisar Dunkin Duniya an samu karuwar waɗanda ke samun magunguna zuwa million 4,idan aka kwatanta da shekarun baya.