1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Cutar Polio ta sake bayyana a Najeriya

Yusuf BalaAugust 12, 2016

Gwamnatin Najeriya ta bayyana sake bullar cutar Polio tun bayan da a ke ganin kasar ta rabu da cutar a shekarar 2014 kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta nunar a ranar Alhamis.

https://p.dw.com/p/1JhFH
Symbolbild Weltgesundheitstag Jedes vierte Baby nicht ausreichend geimpft
Rashin rigakafin na Polio a wasu sassan na Najeriya abu ne da ke samu har yanzuHoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Yara biyu ne a jihar Borno Arewa maso gabashin kasar kawowa yanzu suka sami nakasa ta sanadin cutar a cewar hukumar mai cibiya a birnin Geneva. Ta ce a jihar ta Borno yankuna irin na Gwoza da Jere sun kasance na da wahalar shiga a aikin rigakafin cutar hakan ya sanya sake bayyanar cutar. Abin da a cewarta nakasu ne ga kokarin kasar ta Najeriya na kawar da cutar baki daya, musamman a burinta na ganin bayanta nan da shekarar 2017.

Michel Zaffaran darakta ne a Hukumar Lafiya ta Duniya WHO:

"A jiya mun bayyana samun bullar cutar ta Polio a Arewacin Najeriya, wannan dai ba karamin koma baya ba ne a kokarinmu na kakkabe cutar kasancewar a ranar 24 ga watan Yuli Najeriya ta yi biki na shekaru biyu ba tare da sake bullar cutar ba."

Zaffaran ya ce kawowa ranar Alhamis kasashe biyu ne wannan cuta ke nan daram Pakistan da Afghanistan, yanzu da bayyanar wadannan yara biyu da cutar ta nakasa a kwai masu cutar 21 a duniya a cikin kasashen na Pakistan da Afghanistan da Najeriya.