1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Cutar Zika ta bayyana a Afirka

Yusuf BalaMay 20, 2016

A cewar daraktar yankin na Afirka a hukumar ta WHO Matshidiso Moeti, wannan cuta ta tsallaka daga Amirka ta Kudu zuwa nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/1IrvJ
Brasilien - Forschung Zika Virus - Mikrozephalie
Aikin bincike kan kwayar cutar ZikaHoto: Reuters/P. Whitaker

Kwayoyin cutar Zika da ke janyo haihuwar yara da nakasa ko karamar kwakwalwa da ke bazuwa a kasar Brazil ya zuwa yanzu sun bayyana a karon farko a nahiyar Afirka, abin da ke zuwa bayan zurfafa bincike kan wani samfir na wannan cuta a Cape Verde kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana a ranar Juma'a 20 ga wannan wata na Mayu da muke ciki. A cewar daraktar yankin na Afirka a hukumar ta WHO Matshidiso Moeti aikin binciken gano wannan cuta da aka yi bayan gwajin samfir daga yankin na Afirka ya nuna cewa cutar ta tsallaka daga Amirka ta Kudu inda ta ke bakin kofa a nahiyar Afirka. Moeti ta ce fitar da wadannan bayanai zai taimaka wa kasashen na Afirka su zauna cikin shirin ko ta kwana, sai dai ta ce ya zuwa yanzu ba za a iya cewa a takaita zirga-zirgar al'umma ba saboda tsoron bazuwar cutar.