1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO ta nemi a dage gasar Olympics

Usman Shehu UsmanJune 15, 2016

Kungiyar Lafiya ta Duniya wato WHO ta bayyana cewa akwai bukatar a jinkirta fara gasar Olympics da aka shirya gudanawar a kasar Burazil lokacin bazara sakamon cutar Zika

https://p.dw.com/p/1J6h6
Schweiz WHO David L. Heymann und Bruce Aylward in Genf
Hoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

David Heymann wanda shi ne shugaban kwamitin kwararru na cutar Zika, shi ne ya bayyana hakan, inda ya bayyana cewa akwai barazanar samun cutar ta bazu sakamakon gasar ta Olympics ko da shike ba mai karfi ne ba.

"Kwamitin ya yanke shawarar cewa akwai alama kadan na yiwuwar cutar Zika ta bazu sakamakon gudanar da gasar Olympics da sauran wasanni masu na saba da shi da ke biyo baya. Barazanar ba mai yawa bace, ko kuma ta yiwu ba'a ga yawanta ba sabo da hunturu wanda ya danne cutar a Burazil, kama da ga cikin watannin Agusta da Satumba, bazuwar cutar bashi da yawa ba"

Kwararrun sun kuma bada shawarar cewa kada a dau takunkumin hanawa 'yan Burazil yawo sakamakon cutar. Wassu kwararru kan kiwon lafiya 200, sun bada shawarar a dage gasar ta Olympics, bayan da hukumomin Burazil suka tabbatar samun mutane 1,400 da suka kamu da cutar, wace kudan sauro ke bazawa.