1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WMD: ME AKE CIKI BAYAN KAMMALA YAKIN IRAQI.

January 9, 2004
https://p.dw.com/p/Bvmg
Wasu masana dake aiki a wata jibiya mai zaman kanta a Amurka,sun tabbatar da cewa Shugaban Amurka George W Bush yayi wasan kura da hankulan mutanen duniya wajen bayar da bayanan karya na kandagarkin kaiwa kasar iraqi harin soji.
Masanan na hukumar Carnegie Endowment for international Peace,da suka hada da Jessica mathews da Joseph Cirrincione da kuma George Perkovich sun shaidar da cewa,shugaba Bush na Amurka da kuma wasu hukumonin leken asiri na kasar sun tabbatar da cewa kasar Iraqi nada makaman nukiliya,wanda bisa wannan dalili ne ya haifar kasar ta Amurka ta jagoranci wannan yaki kann kasar ta iraqi.
Abin bakin ciki a nan inji rahoton wadan nan masanan guda uku shine a tun lokacin da aka fara wannan yaki ya zuwa lokacin da aka kammala shi,a kuma zuwa yanzu har yanzu ba,a gano ko samo wadan nan makamai na nukiliya ba a cikin kasar ta Iraqi.
Bisa wan nan dalilin kuwa rahoton masanan mai feji 107 ya bukaci a kafa wata hukuma mai zaman kanta da zata bi kadin baya nan karya da kuma binciko gaskiyar abin da ire iren wadan nan hukumomi na Amurkan suka sani ko kuma suka bayar kann makaman nukiliyar kasar ta iraqi,don tantance ainihin gaskiyar al,amarin.
Bugu da kari rahoton ya kuma bukaci gano gaskiyar sanin dalilin afkawa kasar ta iraqi da yaki da Amurka ta jagoranta, na shin yana da nasaba da siyasa ko kuma kulli kurciyar karin gishiri ne daga wasu hukumomi na leken asiri na kasa da kasa.
A wata sabuwa,binciken da wannan hukuma ta masanan uku ta gudanar ta gano cewa babu wata dangantaka a tsakanin gwamnatin tsohon shugaban kasar ta Iraqi Saddam Hussain da kuma kungiyyar Al,qaeeda,wanda a baya mahukuntan na Amurka keta yadidin cewa suna da Alaqa da juna wajen hada bakin gudanar da hare haren kunar bakin wake.
Har ila yau binciken ya kuma nunar da cewa binciken da sifetocin mdd suka fara a kasar ta iraqi,a baya yafi irin wanda na kasar Amurka sukeyi a kasar ta iraqi bayan kammala yaki a cikin kasar,bisa laakari da abubuwan da suka faru a cikin kasar.
Bisa kuwa irin bayanan da wannan hukuma mai zaman kanta ta samo da kuma irin wanda ta gudanar,ya nunar a fili cewa babu shakka akwai son kai da rashin gaskiya wajen gudanar da wannan yaki kann kasar ta iraqi da Amurka ta yiwa jagoranci.
A yanzu haka a cewar rahoton a tun lokacin da sojojin taron dangi suka samu galabar cafke tsohon shugaban kasar ta iraqi abubuwa sukayi sanyi dangane da batun afkawa kasar da yaki,a hannu daya kuma a sabili da hutun sabuwar shekara da kuma na kirsimeti,kwamitin da aka kafa na binciken musabbabin gaskiyar wasan kurar da mahukuntan kasar ta Amurka sukayi na samun tsaiko na aikin su.
A hannu daya kuwa,a ranar almahis din data gabata mujallar New York Times ta Amurka ta rawaito cewa,A boye mahukuntan na Amurka sun janye dakarun soji 400 daga cikin 1,400 da suka kai izuwa kasar ta Iraqi,wanda aikin su a kasar shine binciken makaman nukiliya na kasar.
Wadan nan dakaru a cewar Mujallar an kashe musu biliyoyin daloli na kudi a tsawon wata da watannin da suka shafe a kasar,ba tare da samo wani cikakken bayani na makaman nukiliyar kasar ba.
Wan nan rahoto na mujallar ya kuma biyo bayan wani a tsakiyar watan di´sambar bara,na matakin da shugaban sifetocin binciken na Amurka ya dauka na barin mukamin sa a karshen watan janairun shekara ta 2004.
David Kay a cewar majiya mai karfi ya dauki wannan matakin ne a sabili da rashin gano abin da ake so a kasar ta iraqi,wanda hakan a cewar hukumar ta Carnegie ya bubar a fili cewa babu wadan nan makamai na nukiliya a kasar ta iraqi.