1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

W.Schäuble ya bayyana rahoton shekara 2006 a game da tsaro a Jamus.

May 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuLT

Ministan cikin gida na ƙasar Jamus Wolfgabng Schäuble, ya gabatar da rahoton shekara da ta wuce, a game da halin tsaro a ƙasar Jamus.

Rahoton ya bayyana abinda ya kira, haɗarruruka guda 2 , da ke matsayin barazana ga kwanciyar hankali a wannan ƙasa.

Babban haɗarin farko, shine hauhawar tsageru, masu tsastauran ra´ayin addinin Islama, a cikin ƙasare ta Jamus.

Ministan Schäuble, ya bada misali, da yunƙurin kai hare-haren da wasu yan takife su ka bukaci abkawa, ga jiragen ƙasa, a watan Juli na shekara bara.

Don magance wannan matsala, hukumomin tsaro na kasa, sun haɗa ƙarfi wuri guda, ta hanyar masanyar bayanai.

Haɗari na 2, inji wannan rahoto, shine ƙaruwar ƙungiyoyin masu aƙidar nazi, wanda kuma su ka shahara ta fannin ƙyamar baƙi.

Ministan Wolfgang Schäuble, ya alkawarta ɗaukar matakan da su ka wajabta, ta hanyar doka, domin taka birki ga masu wannan aƙida.