1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙi a Gaza

Sadissou YahouzaDecember 30, 2008

Rundunar tsaron Isra´ila ta ƙaddamar da gagaramin hari kan zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/GPFx
Ɓarin wuta a zirin GazaHoto: AP


An shiga yini na huɗu tun bayan da Isra´ila ta ƙadammar da gagaramin hari  ta sararin samaniya akan zirin Gaza.

Daga ko ina cikin duniya ƙasashe da Ƙungyiyon ƙasa da ƙasa na cigaba da huruci a game da wannan rikici.

A ƙalla Palestinawa 350 suka rasa rayuka, sannan wasu ƙarin ɗaruruwa suka ji raunua daga farko farkon hare haren na Israe´ila zuwa yanzu.

A daren jiya, rundunar tsaron Isra´ila ta kwan dare tana ruwan harssasai a zirin Gaza.

Ministan tsaron Israela Ehud Barack, ya nunar da cewar bayan hari ta sararin samaniya, na bada jimawa ba, za su ƙaddamar da wani gagaramin harin ta ƙasa da zumar ƙarewa kwata-kwata da Ƙungiyar Hamas dake riƙe da zurin Gaza.

Ministan yayi watsi da kiranye- kiranyen tsagaita wuta dake zuwa daga ko ina cikin duniya.

A yayin da ya ƙara wani saban huruci akan wannan rikici, Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon, yayi kira ga ɓangarorin biyu su dakatar da kaiwa juna hari:Ina kira ga Israela da Hamas su tsagaita wuta, su koma tebrin shawara, sannan su ɗauki dukkan matakan da suka wajaba don kare rayuwar fara hula.

Ko kamin ƙaddamar da wannan hari al´ummomin Gaza na zaune cikin halin ƙuncin rayuwa, saboda haka, shugaban hukumar bada agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya,John Holmes ya kada baki ya na cewa:Akwai matuƙar damuwa a game da taɓarɓarewa rayuwa.

Nan gaba a yau, ministocin harakokin waje na Ƙungiyar Tarayya Turai za su shirya zaman taro na mussamman a birnin Paris na ƙasar France, domin tattanawa akan yaƙin da Isra´ila ta ƙaddamar a zirin Gaza.

rahotani daga Isra´ila sun ambato ganawar da ta hada shugaba Shimon Perez da Firaminsta Ehud Olmert, inda suka tabatar da cewar wanan hare hare tamkar kunnuwa ne jakai na baya, muddun dai Hamas ta cigaba da harba rokoki akan bani yahudu.

A yau da safe, hare haren Iasra´ila,su rugurguza manyan ginunuka guda biyar dake matsayin opisohin ministocin Hamas, da kuma wata jami´ar muslunci a zirin Gaza.

Ƙungiyar Hamas ta yi tsaye kan bakanta na harba rokoki zuwa Isra´ila,wanda daga farkon harin zuwa yanzu suka hallaka yahudawa huɗu.

Daga sassa dabam-dabam na duniya ana ci gaba da zanga zangar nunawa adawa da hare haren na Isra´ila, zanga -zangar mafi girma sun hada dubun dubatar jama´a a ƙasashen Lebanon Yamal Turkiya , Masar.