1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙi da fataucin magungunan jabu a Najeriya

YAHAYA AHMEDNovember 24, 2006

A tarayyar Najeriya dai babu mai nuna shakku kan cewar yawan magungunan da ake sha duk na jabu ne. A shekara ta 2002, hukumar kula da ingancin magunguna wato NAFDAC ta gano cewa kusan kashi 60 cikin ɗari na duk magungunan da ake sayarwa a ƙasar na jabu ne. Wasu ƙwararrun masana fannin sarrafa magunguna na ƙetare ma, gani suke yi, yawan magungunan jabu a Najeriyan ya kai kashi 80 cikin ɗari.

https://p.dw.com/p/BtxK
Shagunan magunguna a bakin titi a birnin Legas, tarayyar Najeriya
Shagunan magunguna a bakin titi a birnin Legas, tarayyar NajeriyaHoto: AP

Kasuwancin magungunan jabu a Najeriya dai na da tsohon tarihi. Wasu alƙaluma na nuna cewa a shekarar 1990, yara ɗari da 9 ne suka mutu, bayan sun sha wani maganin tari. Kazalika kuma a 1996, sai da yara da dama suka mutu bayan an yi musu alluran riga kafi da da wani maganin da aka haramta. Jerin alƙaluma kan asarar rayukan da aka yi a Najeriya, sakamakon shan magungunan jabu dai na da yawa.

Tabbas ne dai cewa, kusan kashi 60 cikin ɗari na magungunan da ake sayarwa a ƙasar na jabu ne, wato ba sa aikin kome, ko kuma suna ɗauke da illoli, waɗanda ke iya janyo asarar rayukan masu shansu. Hakan dai ya sa a wannan huskar, ta harkokin magunguna, kwarjinin Najeriyan ya dusashe ƙwarai a ƙetare.

Akwai dai dalilai da yawa da ke haddasa haɓakar kasuwancin magungunan jabun a tarayyar Najeriya. Da farko dai ’yan fasa ƙwauri ne suka fi yawa a cikin ’yan kasuwan magunguna na ƙasar, sa’annan kuma an daɗe babu wata kafa mai sa ido a hukumance, kan sarrafa magungunan ko shigo da su daga ƙetare da kuma kasuwancinsu.

Amma duk da haɓakar kasuwancin magungunan jabun a Najeriya, ba a nan kaɗai ne ake fama da wannan matsalar ba. Wani babban jami’in Hukumar Lafiya Ta Duniya, wato WHO, Valerio Reggi, ya ce matsalar ta shafi duniya ne baki ɗaya. Gaba ɗaya dai, inji shi, kusan kashi 10 cikin ɗari na duk magungunan da aka sarrafa a duniya na jabu ne. Sai dai ƙasashe masu tasowa ne suka fi huskantar illolin da suke janyowa. Ko me ya sa haka? A ganin jami’in dai:-

„Babbar matsalar ita ce matuƙar talaucin da ake huskanta a ƙasashe masu tasowan. Bugu da ƙari kuma, rashin kyakyawan tsari wanda za a iya aiwatarwa a fannin kiwon lafiya, shi ma na ƙara taɓarɓare al’amura a ƙasashen.“

Duk waɗannan matsalolin dai, a Najeriya ma ana fama da su. Kowa na iya zuwa shagon sayad da maguguna ya sayo kusan duk irin maganin da yake bukata ba tare da wata takarda daga likita ba. To wannan rashin kulawa daga ɓangaren hukumomin ƙasar, na ɗaya daga cikin dalilan da ke janyo bunƙasar kasuwancin magungunan jabun. Wani jami’in Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta taryyar Najeriyan, NAFDAC, Hashim Ubale Yusuf, ya tabbatad da hakan. Amma ya kuma ce, a cikin shekaru 5 da suka wuce dai, hukumarsa ta taka rawar gani wajen fatattakar masu fataucin magungunan jabun. Tsauraran matakan da ta ɗauka sun sa yawan magungunan jabu da dama da ake sayarwa a ƙasar ya ragu da kimanin kashi 80 cikin ɗari. Ko me waɗannan matakan suka ƙusnsa?

„Da farko shi ne shawo kan ma’aikatanmu su nuna ƙwazo da rashin bin son zuci wajen gudanad da aikinsu. To a nan dai mun cim ma nasarar janyo su daga ƙangin cin hanci da rashawa. Na biyu kuma, mun gabatad da wani gagarumin shiri na faɗakad da jama’a, abin da ya sami nasara kuma sosai, saboda yanzu jama’a dama na la’akari da irin magungunan da suke saya. Sun san irin tambayoyin da ya kamata su yi, idan ba su gamsu da irin bayanan da aka ba su wajen sayen magungunan ba.“

Ba dai hukumar NAFDAC ɗin ce kaɗai ke fafutukar yaƙi da yaɗuwar magungunan jabun ba. Har da ma hukumar kwastam, da ’yan sanda. Bugu da ƙari kuma, kafofi kamarsu na kula da kare maslahar jama’a da kuma kamfanonin sarrafa magunguna 92 da ake da su Najeriyan, duk sun ba da nasu shawarwari da gudummowa ga wannan fafutukar. Game da hakan ne kuwa aka sami nasarar da hukumar NAFDAC ɗin ke bayyana wa duniya. Bisa cewar jami’inta Yusuf dai, hukumar za ta iya tabbatar da cewa, a halin yanzu, duk wani maganin jabu da za a samu a ƙasar, to daga ƙetare aka shigo da shi. Ƙasashen da ke kan gaba wajen sarrafa irin waɗannan magungunan kuwa sun haɗa ne da Sin da Indiya da kuma wasu ƙasashen kudu maso gabashin Asiya.

Gwamnatin shugaba Obasanjo dai ta ƙarfafa wa Hukumar NAFDAC ɗin gwiwa wajen gudanad da aikinta. Ta hakan ne ma aka tura jami’ai zuwa Sin da Indiya don su sa ido kan yadda ake sarrafa magungunan da kuma irin waɗanda aka amince a shigo da su Najeriyan. Irin waɗannan matakan dai sun sha a shekarar bara kawai Hukumar ta kame magunguna da dama da aka yi niyyar shigowa da su ƙasar.