1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙi da ta'addanci a Jamus

August 25, 2010

wato kotu ta caji jamusawa uku da laifin haɗa kai da ƙungiyoyin da ke gudanar da ayyukan tarzoma.

https://p.dw.com/p/OwVX
Alƙalan Jamus a kotun birnin KarlsruheHoto: picture-alliance/ dpa

Wata kotun birnin Karlsruhe da ke kudancin Tarayyar Jamus ta tuhumu wasu 'yan kasar da laifin haɗa kai da ƙungiyoyin da ke gudanar da ayyukan tarzoma. Mai shigar da ƙara na wannan birnin ya zargi maza biyu da mace guda da shekarunsu na haihuwa bai fi 31 ba da laifi tallafawa ƙungiyoyin 'yan ta'adda da kuɗi, tare da taimaka musu yaɗa manufofinsu ta kafar sadarwa ta internet.

Tun watan febreru ne aka tsare biyu daga cikinsu, yayin da a ɗaya hannun ake ci gaba da neman shi na ukun ruwa a jallo. Ita wannan kotu ta nunar da cewa tana da ƙwararan shaidu da ke nuna cewa sun taimakawa ƙungiyoyin Jihadil Islami da na Mujahiddin da kuma DTM da hada-hadar kuɗi.

Dokar ƙasar ta Jamus ta haramta yin alaƙa da jerin ƙungiyoyin da gwamanti ta sanyasu a jerin 'yan tayar da zaune tsaye. Alhali ƙungiyoyin uku na jerin waɗanda suka fi ƙaddamar da ayyukan tarzoma a ƙasar Afghanistan.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Ahmed Tijjani Lawal