1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙi tsakanin Isra´ila da Hezbollah

August 10, 2006
https://p.dw.com/p/BunD

Dakarun Isra´ila da na Hezbollah na ci gabada gwabzawa da juna a kudancin Labanon.

A sanarwar da ta hido, rundunar Isra´ila ta tabbatar da yan Hezbolah sun kashe 15 daga cikin sojojin ta a ɓarin wutar da aka yi jiya, wanda kuma ita ce assara sojoji mafi muni, da Isra´ila ta yi, tun farkon wannan yaƙi yau da kimanin wata guda.

Da daren jiya zuwa yau da sahe dakarun Isra´ila sun ci gaba da kutswa a wasu yakunan na kudancin Labanaon inda su ke fuskanatar turjewa daga mayakan Hezbollah.

Hukumomin Isra´ila sun bayana amincewa da ƙara faɗaɗa yaƙin a wasu yanukan na Labanon, da su ka haɗa da karbun kogin Litani.

A jawabin da ya gabatar jiya, shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah, ya bada goyan baya ga aniyar gwamnatin Labanon ta tura dakaru a kudancin kasar.

Nasarrallah yayi kira ga larabawan Haifa da su ƙauracewa matsugunan su, a dalilin shirye shiryen da Hezbollah ke yi, na aika ruwan harssasai zuwa yankunan arewancin Isra´ila.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar sa na na daram!!! , saɓanin

bayanai Isra´ila da ke nuni da cewar Hezbollah ta yi assara fiye da rabi ,na makkaman da ta mallaka.