1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙin Iraƙi ya janyo wani mummnan bala´i maras iyaka

January 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuVU

Shugaban Faransa Jacques Chirac a yau juma´a yayi wani bayani mai tsauri game da mamaye Iraqi da Amirka ta jagoranci yi a shekara ta 2003, yana mai cewa matakin ya janyo rashin zaman lafiya a ilahirin yankin GTT tare da yada ayyukan ta´addanci. Chirac wanda ke yiwa jakadun Faransa jawabin sabuwar shekara ya ce matsalolin da ake fama da su a Iraqi yanzu sun zama shaida na adawar da Faransa ta nuna ga mamaye kasar. Ya ce kamar yadda Faransa ta hango, yakin Iraqi ya janyo wani bala´i wanda har yanzu babu wanda ya san karshen sa. A kuma can Washington shugaba Bush na shirin yin garambawul a rundunar sojin kasar a cikin sabbin manufofinsa game da Iraqi.