1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙin Nahr Al Bared

August 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuDX

Dakarun ƙungiyar Fatah Al Islam sun buƙaci tsagaita wuta, a fafatawar da su ke yi da sojojin gwamnatin ƙasar Libanon tun tsawan wattani 3.

Kakakin ƙungiyar, Abu Salim Taha, yayi kira ga masu shiga tsakanin wannan rikici, su sa baki, wajen cimma yarjejeniya da gwamnati.

Kussan dukkan mazauna yankin Nahr Al Bared,su dubu 40, inda rikicin ya abku sun ƙaurace masa.

Ya zuwa yanzu ,ya rage yan mutane ƙalilan, mafi yawan mata da yayan shugabanin ƙungiyar Fatah Al Islam.

Daga farkon wannan tashe-tashen hankula zuwa yanzu, mutane kussan ɗari 3 su ka rasa rayuka, daga ɓangarorin 2.

A yau ma soja ɗaya na gwamnatin Libanom ya mutu a cikin harbe harbe , kuma shine cikamakon sojojin gwamnati 141 da su ka kwanta dama, tun daga 20 ga watan Mayu, ranar farko ta ɓarkewar rikicin zuwa yanzu.