1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yaɗuwar ƙarancin abinci a Niger

June 5, 2010

Eu ta ce ƙarancin abinci ya kama hanyar zama ruwan dare a Jamhuriyar Niger.

https://p.dw.com/p/NiiR
Hoto: AP Photo

Ƙungiyar gamayyar Turai ta fara nuna fargabarta dangane da ƙamarin da ƙarancin abinci ka iya yi a Jamhuriyar Niger. Kwamishiniyar Eu da ke kula da al'amuran jin ƙai da ta ke ziyarar kwanaki biyu a yankin Maraɗi da matsalar ta fi shafa, ta bayyana cewa ƙarancin abinci ya kama hanyar zama ruwan dare a faɗin ƙasar.

Kristalina Georgieva ta ce a gundumomin Gidan Rumji da Aguie kawai, yaran da ke fama da ƙarancin abinci mai gina jiki ya ninka a cikin watanni tara na baya-bayannan. Kana wasu ƙarin mutane miliyon uku na cikin barazanar faɗawa cikin ja'ibar 'yunwa.

Ƙungiyar ta gamayyar Turai ta ƙara ma hukumomin na Niger ƙarin miliyon 15 na Euro, kwatankwancin biliyon ko miliyar 10 na CFA domin tinkarar matsalar ta ƙarancin abinci. Jamhuriyar ta Niger ta shiga sahun ƙasashen yankin Sahel da fama da ƙarancin abinci ne, sakamakon rashin kyau amfanin gona a bara.

Alƙaluman majlisar Ɗinkin Duniya sun nunar da cewa kashi 70 daga cikin 100 na al'umar ƙasar na cikin barazanar shiga cikin mummunar hali na ƙarancin abinci.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala