1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaɗuwar wutar daji a Rasha

August 7, 2010

Hayaƙin wutar daji ya tirniƙe birnin Moskow da kewaye. Inda yanzu ya tada hankalin mahukuntan ƙasar ta Rasha

https://p.dw.com/p/OehC
Wutar daji a kewayen MoskowHoto: ap

Ƙasar Rasha na fiskantar masifar wutar daji mafi girma a tarihinta, inda a yanzu haka ya tilastawa mutane dayawa barin gidajensu a babban birnin ƙasar Moskow, inda mutane ke sa ƙelle don rufe hancinsu, yayin da yaƙin dake tirniƙe birnin ya ruɓɓan'ya har sau biyar. Yanzu haka dai wutar ta yaɗu zuwa tsakiyar ƙasar yau, yayin da iska mai ƙarfi ke ƙarawa wutar ƙarfi, inda yanzu haka a ƙalla mutane 52 suka mutu. An sauyawa jiragen sama dake sauka a birnin Moskow hanya, don rashin kyawun yanayi. Yanzu haka ana nuna damuwa kan tsaron ƙasar ta Rasha, yayinda wutar ta doshi rubbun makaman nukiliyar ƙasar. Mahukuntan ƙasar suna ƙara damuwa bisa yadda wutar ta nausa yankin yammacin ƙasar, ida aka taɓa fiskatar matsalar sindarin haɗa nukilya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas