1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

YADDA KASASHEN TURAI SUKA KARBI LABARIN HARIN BIRNIN MADRID

YAHAYA AHMEDMarch 11, 2004

Kungiyar kawance ta NATO ta tabbatar wa kasar Spain cikakken goyon bayanta, bayan harin bam din nan da aka kai a kafofin sufurin kasar, a birnin Madrid, inda wasu rahotanni suka ce mutane kusan dari biyu ne suka rasa rayukansu.

https://p.dw.com/p/BvlN
Tutoci a rabin sanda, alamar juyayi, don tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a harin bam da aka kai a birnin Madrid na kasar Spain.
Tutoci a rabin sanda, alamar juyayi, don tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a harin bam da aka kai a birnin Madrid na kasar Spain.Hoto: AP

A cibiyar kungiyar Hadin Kan Turai da ke birnin Brussels, an ta da tutoci a rabin sanda, don tunawa da kuma girmama wadanda suka rayukansu a harin da `yan ta’adda suka kai yau a birnin Madrid na kasar Spain. Shugaban Hukumar kungiyar, Romano Prodi, ya yi kakkausar suka ga harin da cewa:-

"Babu ma wata kalmar da za a iya kwatanta wannan danyen aikin da aka gudanar yau da safen nan a birnin Madrid da ita. A wannan lokaci na juyayi, abin da ya fi muhimmanci ne nuna girmamawa ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma nuna zumunci ga al’umman kasar Spain."

A yau da ranan nan dai, Romano Prodi ya jagoranci wani maci da aka yi a birnin na Brussels don nuna bacin ran jama’a game da harin.

Kwamishinan kula da harkokin kungiyar, daga kasar Spain, Loyola de Palacio, ita ma ta nuna matukar bacin ranta game da harin. Ta bayyana cewa, babu wani abin da ke hujjanta gudanad da wannan danyen aikin, ko wane ne kuma ke ikirarin yinsa. Tana dai matashiya ne da kungiyar `yan awaren nan na Bask, wadda ke fafutukar `yantad da jihar Bask din daga mulkin kasar Spain:-

"Duk Turai na taya Spain makokin wadanda suka rasa rayukansu. Amma mun fi nuna zumuncinmu ne ga tafarkin dimukradiyya, da bin doka da kuma `yancin walwala."

Kazalika kuma, babban jami‘in kula da harkokin ketare na Kungiyar Hadin Kan Turan, Javier Solana, wanda shi ma daga kasar Spain din yake, ya yi kira ga `yan kasarsa da kada su kauce wa zuwa jefa kuri’unsu a ranar lahadi mai zuwa, duk da wannan harin na yau.

"Duk wani bature da kuma duk wanda ya amince da tafarkin dimukradiyya, kamata ya yi, ya yi Allah wadai dda masu gudanad da wannan danyen aikin. Gurinsu ne su hana zaben da aka shirya yi. Sabili da haka ne suka janyo wa dimbin yawan jama’a abin da zai dinga addabarsu."

A cikin nasa jawabin, shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Pat Cox, ya ce wannan harin, hari ne da aka kai kan tafarkin dimukradiyya. Bai kamata, a bai wa `yan ta’adddan damar cim ma gurinsu ba. Game da zaben da za a yi a kasar Spain din a ran lahadi mai zuwa kuwa, shugaban ya kara da cewa:-

"Ku bari a ran lahadi mu ba su amsar cewa, dimukradiyya a kasar Spain ta kafu sosai. Kuma za mu yi duk iyakacin kokarinmu wajen shawo kan ayyuukan ta’addanci."