1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yahudawan Iran

Pick, Ulrich (Istanbul, SWR) May 8, 2008

Akwai kyakkyawar zamantakewa tsakanin Yahudawan Iran da sauran jama´ar ƙasar

https://p.dw.com/p/Dwfg
Shugaban Iran AhmedinejadHoto: IRNA

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da kuma zamantakewa tsakanin al´umomi daban daban a wannan duniya ta mu.

Duk da cewa shugaban Iran Mahmud Ahmedinejad na ƙaryata aukuwar kisan kiyashin da aka yiwa Yahudawa a lokacin yakin duniya na biyu, wato Holocaust to amma a ƙasarsa akwai gamaiyar Yahudawa ta biyu mafi girma a yankin Gabas Ta Tsakiya baki ɗaya. Yahudawa a ƙasar ta Iran suna tafiyar da rayuwarsu ba da wata tsangwama ba inda suke da ´yanci daidai da kowa. Suka ce suna tafiyar da addininsu da sauran al´adunsu ba da wata damuwa ba. Muna ɗauke da ƙarin bayani a cikin shirin na yau wanda ni Mohammad Nasiru Awal zan gabatar.

Madalla: Alƙalumma sun yi nuni da cewa akwai Yahudawa kimanin dubu 25 a Iran. Gabanin ƙaddamar da juyin juya halin Islama a shekara ta 1979 yawansu ya kai dubu 70. Daga cikinsu akwai Moses Saidan wanda ya fi son a kira shi Baban Moses. Wannan mutumin mai shekaru 70 ɗan asalin yankin Isfahan ne dake tsakiyar ƙasar Iran kuma yana da kantinsa sayar da kayakin tarihi da al´adu a layin Ferdausi dake kusa da ofishin jakadancin Jamus dake babban birnin Iran wato Teheran.

1. Moses:

“Ni Bayahude ne mazauni a birnin Teheran. Yanzu ana girmama mu kuma akwai zaman lafiya tsakaninmu da sauran al´ummomi. To sai dai ba haka ya kasance ba bayan juyin juya halin Islama.”

Duk da cewa shugabannin addini a Iran ba su amince da wanzuwar ƙasar Isra´ila ba sannan a kullum shugaba Mahmud Ahmedinejad na nuna ƙyamarsa ga Isra´ila, amma Yahudawa na daga cikin tsirarun da ke da samun cikakkiyar kariya a Janhuriyar ta Islama. Yahudawan Iran kamar sauran tsirarun addinai guda biyu, suna da wakilai a majalisar dokokin birnin Teheran. Baban Moses ya ce su fa Yahudawa ne amma ba masu akidar kafa ƙasar Yahudawa ba. A dangane da abubuwan da suka shafi rayuwarsu a Janhuriyar ta Islama Moses na mai ra´ayin cewa babu wata matsala duk da kalaman nuna ƙyamar Yahudawa da shugaba Ahmedinejad ke yawaita yi.

2. Moses:

“Muna da wuraren ibadar Yahudawa kimanin guda 20 a nan Iran. Kuma muna tafiyar da addininmu ba da wata tsangwama ba. A yankin Isfahan alal misali muna da maƙabartarmu. Kuma a baya bayan nan an gano wani dutse da ya kai shekaru dubu 3. Haka dai abin ban sha´awa ne.”

A matsayinsu na wata gamaiyar addini, Yahudawa sun riga musulmi zuwa Iran fiye da shekaru dubu. Kasancewarsu a yankin ya samo asali ne tun bayan kame yankin Babylon a shekara ta 539 gabanin haihuwar Annabi Isha (ASW). Yayin da wasu ´yan yankin Hebrew suka koma Falasɗinu bayan an sake su daga kurkuku, wasunsu sun ci-gaba da zama cikin wannan daula ta Babylon.

3. Mace:

“Gaskiya mu a nan Iran ba mu da wata matsala da Yahudawa. Dole ne a bawa tsiraru dake cikinmu ´yancin rayuwa kuma bai kamata a dame su. Kawo yanzu ban ji wani abu mai kama da tursasa musu ba.”

Lalle babu mamaki da Moses ke tattare da ƙwarin guiwa. Domin yana da cikakkiyar masaniya kan yadda rayuwar yankin ta ke. Alal misali a lokaci yaƙin Iran da Iraqi a cikin shekarun 1980, Isra´ila ta turawa Iran makamai a asurce bisa dalilan cewa dukkansu biyu suna yaƙi ne da ne Larabawa. Yahudawa Iran dai na da wani matsayi na musamman inda ake ba su izinin kai ziyara Isra´ila.

4. Moses:

“Haka ya ke yanzu. Amma a shekaru takwas na farkon juyin juya hali ba a ba mu wannan izini ba. Yanzu kam ba da wata matsala ba muna iya zuwa Isra´ila mu kuma dawo. Hasali ma tsohon shugaba Khatami na da kyakkyawar hulɗa da Yahudawa.”

To sai dai abin da Moses bai faɗa ba shi ne suna wannan tafiya ne ta wata ƙasa musamman ta Turkiya. A Iran dai ana bambamtawa tsakanin Yahudawa da kuma masu ra´ayin kafa ƙasar Isra´ila.

5. Na miji:

“A haƙiƙa kamar sauran ´yan Iran ni ma ba ni da wata matsala da Yahudawa. To amma dukkanmu muna da matsala da masu ra´ayin kafa ƙasar Yahudawa. Ai a cikin Alqur´ani ma an ƙarfafa batun girmama Yahudawa da Kiristoci.”

Har yanzu ´yan Iran ba su da cikakkiyar masaniya game da kisan kare dangi da aka yiwa Yahudawa da ake yiwa laƙabi da Holocaust. Saboda haka ne ma ba a wani nuna damuwa a cikin ƙasar ba lokaci da shugaba Ahmedinejad ya kwatanta kisan ƙare dangin da wata al´amara.

6. Na miji:

“Kisan ƙare dangin na Holocaust wani abu ne da ake yawaita yaɗa jita-jitar sa. Ni ban yarda da aukuwarsa ba. Duk da cewa muna son Yahudawa a tsakaninmu, amma mun tsana kuma mun tir da kafa ƙasar Isra´ila da waɗanda suka taimaka aka kafa ta.”

To sai dai tun a ƙarshen shekarar da ta gabata abubuwa sun fara canzawa. Ganin yadda Iran ta yi ƙaurin suna wajen ba wa duniya mamaki, gidan telebijin ƙasar ya fara watsa wani jerin wasan kwaikwayo dangane da kisan na Holocaust, abin da ya janyo cece-kuce da suka daga wasu ´yan ƙasar.

7. Sauti:

Wasan mai rukunai 16 ya ƙunshi tarihin soyayya tsakanin wani ɗan Iran Habib Parsa wanda a lokacin da yake karatu a birnin Paris a cikin shekarun 1940 ya haɗu da wata Bayahudiya ´yar Faransa da ake kira Sarah. Jim kaɗan sai sojojin Jamus suka mamaye babban birnin na Faransa kuma suka fara fatattakar Yahudawa. Parsa bai wata-wata ba sai ya fara tattaunawa da jami´an diplomasiyar Iran waɗanda suka taimaka aka kwashe Sarah da iyalinta da sauran Yahudawa zuwa Teheran. Matasan Iran dai suna matuƙar sha´awar wasan kwaikwayo.

8. Matashi:

“Wannan shi ne karon farko da muka ga wani fim da ya nuna mawuyacin halin da Yahudawa suka shiga ciki. Fim ɗin yana da ban sha´awa musamman ga waɗanda ba su da masaniya dangane da kisan ƙare dangi na Holocaust.”

Duk da cewa ɗaukacin ´yan Iran ba sa ƙyamar Yahudawa kamar yadda furuce-furucen shugabansu ke yin nuni, amma nan gaba kaɗan yawan Yahudawa a Iran zai ragu, musamman saboda ƙaruwar masu tsattsauran ra´ayin addini. To sai dai duk da haka in ban da Isra´ila, Iran ta fi kowace ƙasa a yankin Gabas Ta Tsakiya yawan Yahudawa, inda suke zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka da sauran mabiya addinai kamar musulmi da kiristoci.