1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yahya Jammeh ya kafa dokar ta baci

January 17, 2017

Shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh ya kafa dokar ta baci,daf da lokacin da wasu karin ministoci guda hudu na kasar suka yi marabus.

https://p.dw.com/p/2Vx8B
Gambia Yahya Jammeh Präsident
Hoto: Reuters/C. G. Rawlins

Lamarin ya biyo bayan  yunkurin sassanta rikicin cikin ruwan sanhi da Kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta gaza cimma wacce ke shirin daukar matakin yin amfani da karfin soji.A halin da ake ciki rahotannin daga kasar ta Gambiya na cewar gwamnatin ta Jammeh na ci gaba da tsare wasu sojojin wadanda ba su amince ba da shugaban ya ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki.A ranar Alhamis mai zuwa yakamata shugaba Jammeh ya sauka ya mika mulki ga Adama Barrow mutumin da ya lashe zaben wanda yanzu haka yake yin hijara a Senegal.