1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aiki a kasar Cadi

Yahouza sadissouAugust 16, 2005

Kungiyar yan jarida a kasar Cadi ta kudurci shiga yajin aiki don kalubalantar hukunce-hukuncen dauri na barkatai da kotuna ke yan kewa ga yan jaridar kasar

https://p.dw.com/p/BvaR

Kungiyar yan jarida ta kasar Cadi UJT, ta yanke shawara shiga yajin aiki , daga ranar 22 zuwa 26 ga watan da mu ke ciki, a sakamakon ukuba, da azaba, da hukumomin kasar ke, nuna wa yan jarida a cikin aikin su.

Shugaban kungiyar UJT, da ya bada labarin ya bayana cewa, wannan yajin aiki, ya shafi yan jarida masu zaman kan su, da na gwamnati, don nuna hadin kai, ga abokan aikin su, da kotu ta yanke wa hukunce- hunkuncen dauri.

Ranar jiya litinin, kotu ta gurfanar da Madame Sy Koumbo Singa Gali, daraktar jaridar L` Observateur, tare da tuhumar ta da buga labarun karya, da kuma tada zanga zanga cikin kasa.

Sakamakon wannan shari`a ta yanke mata, hunkunci daurin shekara guda, a kurkuku da kuma tara ta CFA jika dari 2, wato kimanin Euro 305.

A kwanakin baya ne, jaridar L´observateur ta yi hira da Ngarhode Jarma, wani manazarcin harakokin siyasa, a kasar Cadi, inda ya danganta larabawan Cadi, da yan janjawid wato yan yakin sa kan nan, na Sudan, da su ka hadasa mace- mace a yankin Darfur..

Shi kansa, wanda yayi kalamomin, a ranar 18 ga watan yuli da ya wuce, kotu ta yanke masa hukunci dauri shekaru 3.

Bugu da kari, hukumomin Cadi, na tuhumar Jarma, da rubuta wata kasida, a game da zaben raba gardama da a ka yi a kasar Cad,i a watan juni da ya wuce, wanda a sakamakon sa, Idriss Deby ya samu damar shiga takara a zaben shugaban kasa mai zuwa.-

A cikin kasidar, marubucin yayi suka da kakkawasar halshe, ga wannan mataki, da ya tabatar da cewa ,ya sabawa dokokin kasar cadi.

Ranar 8 ga wanan wata da mu ke ciki, kotu ta kara yanke hukunci daurin watani 6, ga wani dan jarida, mai suna Mishel Didana, tare da zargin sa, da tada fitina cikin kasa, bayan ya yi rahoto a game da yan tawayen Sudan, da ke kan iyakar Cadi.

Sannan kotu, ta yanke hunkunci a watan da ya gabata, ga karin wani dan jarida na l`Observateur, mai suna Ngaradumbe Samory, bayan ya wallafa wata wasika da yan kabilar arewa maso gabacin kasar, su ka rubuta, inda su ka bukaci a yi belin yan uwan su da a ka kama.

A dalili da wannan hukunce- hukunce na barkatai- kungiyar yan jaridar cadi- ta yanke shawara shiga yajin aiki.

Kungiyoyin kare hakokin yan jarida na dunia, kamar su „Reporter sans frontieres“ tunni! sun yi suka da babban mirya ga yanayin da gwamnnatin Cadi ta saka yan jarida.

A nasu bangare, hukumomin Cadin, na kariya kansu ,da zargin da a ke masu, na sa takunkumi ga yan jarida.

Ministan sadarwa na kasar, ya sanar cewa, wannan matakai bai sabawa dokoki ba.