1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aiki ya gurgunta kamfanin Lufthansa na Jamus

Suleiman BabayoSeptember 8, 2015

Matuka jiragen saman kamfanin Lufthansa na Jamus sun nuna rashin jin dadi game da sabbin matakan da kamfani ya dauka wanda ke haifar da takaddama.

https://p.dw.com/p/1GTI6
Deutschland Streik der Lufthansa-Piloten
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Balk

A wannan Talata yajin aiki matuka jiragen saman kamfanin Lufthansa na kasar Jamus ya gurgunta harkokin tafiye-tafiye. Tuni kungiyar matuka jiragen saman ta kai kamfanin kara saboda shirin daina daukan sabbin matuka jiragen sama karkashin dokokin gata na kwadago a Jamus.

Mai-magana da yawun kungiyar ya ce baya ga Talata da Laraba akwai yuwuwar kafin karshen mako a sake wani yajin aikin. Tuni kamfanin na Lufthansa ya soke tafiye-tafiye jiragen sama masu nisa 84 daga cikin 170, sannan akwai yiwuwar soke kashi biyu bisa uku na tafiye-tafiyen jiragen saman na ranar Laraba. Kamfanin

Lufthansa na Jamus ya kasance daya daga cikin jiga-jigan kamfanonin jiragen sama a duniya. Sai dai wannan yajin aiki bai shafi sauran da suke karkashin kamfanin Lufthansa kamar Germanwings da sauransu ba.