1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aikin gama gari a Nijeriya

November 10, 2010

Ma'aikata a Nijeriya sun fara yajin aikin gama gari na neman ƙarin albashi

https://p.dw.com/p/Q3WS
Shugaban Nijeriya Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/dpa

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago a Nijeriya ta sanar da shiga cikin yajin aiki akan neman ƙarin albashi kamar yadda ta tsara a yau Laraba, jim kaɗan bayan ganawar da shugabannin ƙungiyar suka yi tare da shugaba Goodluck Jonathan na ƙasar. A jiya ne dai shugaban na Nijeriya ya katse wata ziyara a Legas domin ganawa tare da shugabannin manyan ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar guda biyu, wato NLC da kuma TUC.

A ƙarshen taron, wanda ya gudana a jiya da daddare, shugaban tawagar ƙungiyar ƙwadago a wajen ganawar ya ce ma'aikata a Nijeriya za su ci gaba da yin yajin aikin duk kuwa da buƙatar jinginar da shi da shugaba Jonathan ya gabatar, yana mai ƙarawa da cewar, ma'aikatan za su janye yajin aikin ne kawai bayan taron haɗin gwiwa na kwamitocin zartarwar ƙungiyoyin. Muƙaddashin shugaban ƙungiyar ƙwadago a Nijeriya ta NLC Promise Adewusi ya shaidawa manema labarai bayan ganawa da shugaban ƙasar cewar, yajin aikin zai ci gaba, ba tare da wani ɓata lokaci ba har sai kwamitin zartarwar ya sake bayar da sanarwar janye shi.

Ƙungiyar ƙwadagon ta amince da Naira dubu 18 a matsayin mafi ƙarancin albashin da ma'aikaci zai karɓa a Nijeriya bayan tunda farko ta nemi Naira Dubu 52, amma daga baya kuma gwamnati ta ce ba za ta iya ma biyan dubu 18 ɗin ba.

In anjima kaɗan ne shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon za su gana domin duba mataki na gaba da za su ɗauka wato ko dai janyewa ko kuma ci gaba da yajin aikin gargaɗi na kwanaki ukkun.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu