1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aikin jiragen kasa a Faransa

Zainab MohammedNovember 18, 2007
https://p.dw.com/p/CIZs

Ma’aikatan jiragen kasa na kasar Faransa,sun faɗada yajin aikin da suke gudanarwa har yaa zuwa gobe litinin,adangane da adawarsu da yanke kudaden pension da gwamnati ke shirin yi.A jiya asabar dai jirgi ɗaya,daga cikin masu sauri na TGV ne yayi aiki,ayayinda jirage kalilan ne sukayi aiki daga cikin na parinja ,musamman waɗanda ke zirga zirga a birnin Paris.Prime ministan Faransa Francois Fillon,yayi furucin cewar kamfanin jiragen Ƙasar ta SNCF mallakar gwamnati,zata iya cimma sasantawa,idan har ta janye wannan yajin aiki.A tarayyar jamus kuwa,jiragen kasa sun fara aiki bayan yajin aiki na tsawon sa’oi 62 da suka gudanar.A’yan watanni da suka gabata dai matuka jiragen kasar na jamus,sun bukaci kamfanin jiragen na Deutsche Bahn data kara musu albashi.