1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

yajin aikin jiragen kasa a jamus

July 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuHP

Pasinjoji dake amfani da jiragen kasa zasu fuskanci matsalolin tafiye tafiye daga gobe jumaa,sakamakon zartarwa da manyan kungiyoyin maaikatan jiragen sukayi na gudanar da yajin aiki na gargadi.Wannan zaratarwa dai ya biyo bayan cimma daidaito dangane da bukatar karin albashi a bangaren maikatan jiragen kasan.Kamfanin Deutsche Bahn dake da jiragen kasa a nan jamus dai tayi watsi da bukatun kungiyoyin na karin albashin kashi 7 daga cikin 100,na abunda ake biyansu yanzu,inda ta amince da kashi biyu kachal.Babbar kungiyar maaikatan jiragen kasar ta GDL dai na bukatar karin kashi 31 daga cikin 100 na albashinsu,ayayinda suka bukaci hukumar gudanarwan kamfanin data biya dorebobi nasu kudaden albashi daban.