1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yajin aikin ma'aikatan kafofin yaɗa labarai a Nijeriya

November 22, 2010

Ma'aikatan kafofin yaɗa labaran na yajin aikin gama gari ne domin gargaɗi ga hukumomin ƙasar dangane da neman ƙarin albashi.

https://p.dw.com/p/QFKZ
Shugaba Jonathan GoodluckHoto: AP

A yau ne ƙungiyar 'yan jarida ta ƙasa a Nijeriya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar ma'aikatan Rediyo da na Telebijin da kuma wasannin al'adu a Nijeriya suka shiga yajin aikin gama gari na yini ukku domin neman ƙarin albashi daga hukumomin ƙasar. Ƙungiyoyin dai suna neman hukumomi su biya su mafi ƙarancin albashin naira dubu 82 ne dai dai da sakamakon wani rahoton kwamitin da hukumomin Nijeriya suka ƙafa akan albashin ma'aikatan gidajen rediyo da telebijin a ƙasar ya ƙayyade.

Ma'aikatan suka ce ba su da wani zaɓi illa tsunduma cikin yajin aikin, bayan gazawar tattaunawar da suka yi ta yi da jami'an gwamnatin Nijeriya. Yajin aikin ma'akatan gidajen rediyo da telebijin da kuma na jaridar dai, ya zo ne bayan yajin aikin gargaɗin da ƙungiyar ƙwadagon ƙasar ta yi - ita ma akan neman ƙarin albashin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Mohammed Abubakar