1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki a kasar Chadi

December 21, 2006

Tun watanni da dama da suka wuce kasar Chadi ke fama da yaki

https://p.dw.com/p/Btww
Idriss Deby
Idriss DebyHoto: AP

A watan afrilun da ya wuce, kadan ya rage ‘yan tawayen Sudan su kifar da gwamnatin Chadi domin kuwa dakarun na sa kai sai da suka yi wa fadar shugaba Idriss Derby kawanya a N’Djamena. Shugaban ya samu kafar tsallake rijiya da baya ne sakamakon hare-haren jiragen sama da tankokin yakin Faransa. Tun kuwa daga wancan lokaci aka kafa dokar ta bace a kasar Chadi. Kuma a wannan halin da muke ciki yanzu al’amuran rayuwa sun canza, ba kamar yadda aka saba yau da kullum a kasar ba in ji wani dan Chadin da ake nemi jin ta bakinsa:

“Wannan matsalar ta kada zukatan illahirin al’umar kasa. Duk kowa da kowa na cikin fargaba da zaman dardar. Da kyar mutum ke iya fita zuwa bakin aikinsa. Domin kuwa sai da suka shigo mana a cikin watan afrilun da ya wuce kuma tun daga sannan al’amura suka canza suka dauki wani sabon salo. An fuskanci hadarurruka da asarar rayuka da dama. Ina cikin damuwa matuka ainun. Ko da yake ni kan shigo gari, amma ina tattare da fargaba.”

A hakika tun abin da ya kama daga farkon shekara ake fafata kazamin yaki tsakanin sojan kasar Chadi da ‘yan tawayen Sudan kuma talakawan kasa sune suka fi fama da radadin lamarin. Miliyoyin jama’a suka tagayyara a lardin Darfur, a baya ga wasu dubban daruruwan da aka kashe ba tare da KTT ko MDD ko kuma KTA sun yi katsalandan ba saboda kiyawar da fadar mulki ta Khartoum tayi bisa ikirarin cewar wai ba ta so a yi mata shisshigi a al’amuranta na cikin gida. Ita kanta Chadi a yanzu haka tana da sama da ‘yan gudun hijira dubu 70 da suka barbazu a duk fadin kasar. A takaice kurar rikicin Sudan ta fara yaduwa domin ta mamaye yankin tsakiyar Afurka. To sai dai kuma kamar yadda masu iya magana su kan ce ne idan an yi ta barawo sai kuma a yi ta mabi sau. Domin kuwa shi kansa shugaba Idriss Derby yana da rabonsa na alhakin wannan mummunan ci gaba. Shugaban dai ya dare kan karagar mulki ne sakamakon zabe na demokradiyya, amma a daya bangaren har yau yana kunnen-uwar-shegu a game da shirya wani sabon zabe a kasar ta Chadi. Kazalika a yayinda yake yakar ‘yan tawaye masu samun daurin gindi daga gwamnatin Sudan, a daya hannun kuma yana bakin kokarinsa wajen murkushe dukkan abokan hamayyarsa a cikin gida tare da daukar tsauraran matakai na tace labarai, in ji wani dan jaridar kasar mai suna Jean-Claude Nekim, wanda ya kara da cewar:

“Ina fama da haushi da takaici, saboda ba ni da ikon tafiyar da aikina kamar yadda na saba a cikin shekaru 15 da suka wuce. Yau da sanyin safiya sai da na hallara gaban kwamitin tace labarai, wanda ya daddatse rahoton da na rubuta. A halin yanzu haka ina tababa a game da ci gaba da wannan aiki. Sannu a hankali dai yanayin siyasa na canzawa zuwa mulki na kama-karya.”