1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman karin tallafi a yaki da Boko Haram

Ubale Musa/YBMay 15, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa kawancen kungiyar ta Boko Haram da mayakan IS na zama babbar barazana ga tsaro na daukacin kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/1Io6Z
Nigeria Boko Haram Krisengipfel Francois Hollande und Muhammadu Buhari
Shugaba Francois Hollande da Muhammadu Buhari a taron koli kan tsaro a NajeriyaHoto: Reuters/A. Sotunde

Bayan share tsawon lokaci suna babban taro a Abuja, akalla shugabannin kasashen Tafkin Cadi da 'yan uwansu makobta da ma Turawan da ke kawance a cikin yakin dai sun zartar da hukuncin ci gaba a kokarin kai karshen matsalar komai runtsi.

Duk da cewar dai sun nasarar sauyin matsayi ga kungiyar da a baya ke rike da yanki babba cikin kasar zuwa ga mai fafutikar kare kanta a dajin Sambisa a yanzu, kasashen sun ce ba su da niyar saurarawa har sai sun tabbatar da kai kungiyar zuwa gidan tarihi.

To sai dai kuma ra'ayi ya zo guda ga bukatar mai da hankali ga kokari na sake ginin yankin da maida rayuwa mai amfani da nufin kaucewa sake bullar matsalar da ta kai su dare a halin yanzu.

Nigeria Boko Haram Krisengipfel Francois Hollande und Muhammadu Buhari
Shugaba Hollande da Buhari na karbar gaisuwar ban girma a AbujaHoto: Reuters/A. Sotunde

Abun kuma da a fadar mai masaukin bakin kuma shugaban tarrayar Najeriya Muhammadu Buhari zai dauki hankali daga yanzu.

"A matsayin daya daga cikin hanyoyin warware musabbabin ta'addancin da kuma akidar gaba, dole ne mu samar da ingantancen tsarin kyautata rayuwa bayan yakin, sannan 'yangudun hijira ya zuwa gidanjensu cikin zaman lafiya da mutuncinsu."

Shi ma dai babban bakon taron kuma shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya ce kungiyar har yanzu Boko Haram na zaman barazana ga duniya baki daya.

Taron na Abuja dai ya zamo danba ta agaji na kudade da nufin fara aikin gyaran da ya baci tare da Tarayyar Turai ta sanar da agajin Euro miliyan 40 ta wannan fuska. Ita ma dai Birtaniya ta ce ta na shirin kashe Fam na kasar har miliyan 32 cikin shekaru uku da ke tafe da nufin samun nasarar kyautata rayuwa ta al'ummar yankin.

Nigeria Francois Hollande trifft den nigerianischen Außenminister Geoffrey Onyeama
Shugaba Hollande lokacin da ya isa NajeriyaHoto: Reuters/A. Sotunde

To sai dai kuma daga dukkan alamu har yanzu da sauran tafiya a tunanin Kashim Shettima da ke zaman gwamnan Borno jiha mafi ji a jiki a cikin rikicin.

In har taimakon ya yi kadan, a cewar Injiniya Sunusi Imrana Abdullahi da ke zaman sakataren hukumar kula da Tafkin Cadi, Turawan na da taimako na kwarewa da za su bayar a yankin.