1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

YAKI DA CUTAR AIDS A KASAR ZAMBIA:

JAMILU SANI:March 9, 2004
https://p.dw.com/p/BvlR
Shugaban kasar Zambia Levy mwanawasa ya fuskanci matsaloli na rashin fahimtar juna tsakaninsa da kungiyoyin bada agaji na duniya na,tun bayan da ya kama ragamar mulkin kasar ta Zambia.
Dangantka tskanin shugaban kasar ta Zambia da kungiyoyin bada agaji na masu zaman kansu na duniya ,ta fara tsami ne bayan da shugaban kasar ta Zambia ya zargi kungiyoyin dake yaki da cutar Aids da laifin karkata alkalar kudaden da aka samu na taimako wajen yaki da cutar Aids wajen biyan bukatun kansu.
Zargin dai da Muwanawasa ke yiwa kungiyoyin na bada agaji masu zaman kansu ya kara ta'azara ne bayan da ya fara sukan lamirin ministar raya karkara da kuma jin dadin jama'a ta kasar Marina Nsingo a dagane da irin tafiyar hawainiya da ake fuskanta a dukanin shirye shiryen da aka sanya a gaba wajen yaki da cutar Aids a kasar ta Zambia.
A halin da ake ciki dai ministar raya karkara da kuma kyautatuwar jin dadin jama'a ta kasar Zambia Nsingo,ta yi nuni da cewa alumar kasar Zambia sun rigaya sun dawo daga rakiyar kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa masu zaman kansu,sabili da har kawo yanzu sun gaza yin wani abin ku zo mu gani wajen yaki da kangin talauci da alumar Zambia ke fama da shi a halin yanzu,baya kuma ga anobar cutar Aids data raigaya ta zama ruwan dare gama duniya a wanan kasa ta kudancin Africa.
A yanzu haka dai akwai kimanin kungiyoyin bada agaji masu zaman kansu a Zambia,wanda kuma duka da yawan su a kasar,sun gaza gudanar da aiyuka na cigaba har suka kai 450 a yankunan karkarar kasar,ciki kuwa da yunkurin da aka sanya a gaba na yaki da mugunyar cutar Aids mai karya garkuwaar jiki.
Muwanawasa ya shaidawa mahalarta baban taron yaki da cutar Aids na kwanaki biyu da ya sami wakilicin jami'an majalisar dikin duniya da kuma wasu yan majalisar ministoci daga kasahen kudancin Africa,cewa yawancin kungiyoyin bada agaji masu zaman kansu na kasa da kasa nada kudade da suka samu na taimakon yaki da cutar Aids a hanun su,ammman kuma sun gaza daukar matakan da suka dace a wanan fuska. Shugaban kasar dai ta Zambia ya zargi majalisar dinkin duniya da laifin goyon bayan a baiwa kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa taimakon dukanin taimakon kudaden da aka samu na yaki da cutar Aids.
Shi kuwa Peter Piot daractan shirin yaki da cutar Aids na majalisar dinkin duniya cewa yayi irin wana hali na rashin fahimtar juna dake samu tsakanin kungiyoyin bada agaji masu zaman kansu na kasa da kasa da gwamnatin Zambia a dangane da batun shirin yaki da cutar Aids,ba komai zai yi ba face haifar da rudani wajen yadda za'a kashi irin kudaden da aka samu na taimako wajen yaki da cutar ta Aids.
Mwanawasa ya furta cewa gwamnatin Zambia nada zababun wakilai da ya zasu rika lura karbar kudaden da aka samu na taimakon yaki da cutar Aids,fiye da kungiyoyin bada agaji masu zaman kansu na kasa da kasa,domin kuwa koda taka je ta zo su din dai za'a tambaya yadda aka kashe irin wadanan kudade.
A lokacin da shugban kungiyoyin bada agaji na duniya ya ziyarci kasar Zambia farkon wanan watan,Mwanwasa ya shaida masa cewa kungiyoyin bada agaji na duniya dake kasar sun zamanto,tamkar yan jama'iyar adawa mai makon a ci yanuwa ne da hada kai da su wajen ciyar da kasar gaba.
Mai magana da yawun kungiyoyin yaki da cutar Aids a zambia Benson Changuta cewa zargin da Muwanawasa ke yiwa kungiyoyin bada agaji na duniya dake kasar bashi da wani tushe balantana makama.
Wanan dai shine karo na farko da gwamnatin zambia ta zargi kungiyoyin bada agaji masu zaman kansu na duniya da laifin satar kudaden da aka ware don taimakon matalautan kasahe masu tasowa na Africa.