1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da shan miyagun gwayoyi a Najeriya

Abdulrahman Kabir | Gazali Abdou Tasawa
December 19, 2017

A ci gaba da neman hanyoyin magance matsalar sha da fataucin kayan maye a arewacin Najeriya, majalisar dattawan kasar ta shirya taron masu ruwa da tsaki kan matsalar da fito da shawarwari na shawo kanta.

https://p.dw.com/p/2pdkx
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture alliance/NurPhoto

Majalisar dattawan Najeriya ta shirya wannan taro ne sabili da damuwa da bayyana alkalumma na matasa maza da mata da suke jefa kansu cikin mummunar tabi'a da ta ke neman lalata rayuwarsu baki daya. Da ya ke jawabi a gurin wannan taro da ya gudana a birnin Kano Shugaban majalisar datawan Najeriyan Bukola Saraki ya yi karin bayani kan girman matsalar yana mai cewa "a baya bayan nan wannan tabi'a ta shan kayan maye na ci gaba da zama abin damuwa ta la'akari da yadda ta ke kara saurin yaduwa a cikin jihohin Najeriyar ta Arewa."

Shugaban na majalisar dattawan Najeriya din ya ce majalisar ta yanke shawara ba da tata gudunmawar ce domin samo hanyoyin magance matsalar wacce ke addabar makomar manyan goben a wannan yanki.

Dr. Dora Akunyili NAFDAC Kontrollbehörde Lebensmittel Medikamente Labor Analyse Nigeria
Hoto: Getty Images/P.Ekpei

Shi ma dai dan majalisar wakilai ta Najeriyar daga jihar Jigawa Malam Sani Zoro ya nuna damuwarsa ce da yadda ake samun 'yan Najeriyar da hannunsu dumu-dumu a harakar fataucin miyagun kwayoyi a kasashen ketare, lamarin da ke bata sunan Najeriyar inda ya ce "kowane lokaci idan ku ka duba bayan duk watannin uku ko hudu za ka ji cewa an rataye wasu 'yan Najeriya  a Pakistan ko Malesiya ko Indunusiya wadanda ke safarar wadannan kwayoyin da ke neman kassara masu mutane"

A lokacin wannan taro jami'an hukumomi daga sassa daban-daban na Najeriya da ke da ruwa da tsaki wajen yaki da kayan mayen, sun fito da illolinsu da alkalumman matasan kowace jiha da suke illata wa rayuwa.