1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

YAKI DA TAADANCI

ZAINAB AM ABUBAKAR.November 13, 2003
https://p.dw.com/p/Bvnd
Dayake jawabi wa wakilan wata hukuma dake fafutukan neman Democradiyya a farkon wannan wata,shugaba Bush na amurka ya jadda manufarsa na ganin cewa Democradiyya ya zamu gindin zama a yankin gabas ta tsakiya.Yace idan har baa kwato yankin daga halin da take ciki na mulkin danniya ba,babu wani cigaba da zaa samu a wannan yankin.Wadannan kalamai na Bush sun zo adai dai lokacin alummar duniya ke tofa albarkacin bakinsu tare da yiwa manufofin ketare na Amurka suka,musamman a dangane da yanayi da ta tsoma kanta na abunda ta kira yaki da taaddanci.

A halin da ake ciki yanzu dai kasahen Afganistan da Iraki na cikin halin ni yasu,kana Amurkan na kira ga kasashen musulmi dasu dubeta da idanun rahama,ayayinda a hannu guda kuma musulmi ke ganin cewa yaki da taaddanci da ake ikirari ba komai bane face yaki da musulunci kai tsaye. Wadannan matsaloli sun fara bayyana shakku dangane da samun nasaran shugaban na amurka a zaben da zai gudana a shekara mai zuwa,inda yake fatan zarcewa kann wannan kujera tasa.Wanda ke bukatar ababi da dama kafin ya cimma burinsa.Da farko dai dole ya tabbatar wa alummar Amurka wadannan tsare nasa wanda zai tabbatar dacewa dukkan wadannan lamura dayake gudanarwa suna bisa kaida kuma sunada ga muhimmanci.

Dole ne ya tantance dalilansa na afkawa Iraki da yaki,tunda ahalin yanzu maganar makamai masu guba ya zama tsohon labari tunda ya zuwa wannan lokaci baa gano komai ba.Tunda kuma a fadinsa yaki da taaddanci na nufin samarda mulkin democradiyya a yankin gabas ta tsakiya amma ba kwadayin albarkatun mai ko kuma marawa Izraela baya,dole ya tabbatarwa yankin cewa saboda alheri yake nemansu dashi. Bugu dakari tunda yanzu gwamnatin Amurak ta gano bakin jini da duniyar musulmi ke kallonta dashi ,don haka abunda zai iya fisshe ta shine ta janye kanta daga gwamnatocin kasashen musulmi.

Kazalika ga matsalar yankin palasdinawa,wadda Amurka na daga cikin wadanda suka amincewa daftarin bawa palasdinawan yantacciyar kasarsu a shekara ta 2005,amma ahalinda ake ciki yanzu tana kasa tana dabo.Mahmud Abbas ya kasance tarihi ayayinda Yasser Arfat ke cigaba da rike madafan Iko.

Dangane da manufofin ketarenta bayan harinda aka kaimata a watan satumban 2001 kuwa,wasu kasashen musulmi sun samu matsin lamba daga Amurka musamman Pakistan,da saudi Arabia.

Syria ta marawa Amurka baya akan Iraki ,Malasia ta amince da majalisar Irakin da Amurkan ta nada,tare da gayyatansu zuwa taron kasashen musulmi a watan daya gabata.Iran ta amince da bada bayanan harkokinta na makamasi.To amma ayar tambaya anan itace,Amurka zata cimma burinta na tilastawa ire iren wadannan kasashe amincewa da mulkin democradiyya kuwa? Hakika dole ne suma kasashen Larabawan suga zahirin wannan batu,tare da hade kawunansu wuri guda ,domin sai bango ya tsage kadangare kann samu wurin shiga.