1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da zazzabin cizon sauro a duniya.

April 25, 2017

Hukumar lafiyar ta duniya za ta gudanar da gwajin allurar rigakafin Malaria a kasashen Kenya da Malawi da kuma Ghana.

https://p.dw.com/p/2bt0b
Tropische Tigermücke Aedes albopictus
Hoto: Imago

Yau ce ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro na duniya, ranar da hukumar lafiya ta duniya ta kebe domin yaki da cutar a doron kasa.

Hukumar lafiyar ta duniya ta kuma sanar da cewa za'a fara gwajin allurar rigakafin cutar karon farko a badi a kasashen Kenya da Malawi da kuma Ghana.

Allurar rigakafin mai suna RTSS ana sa ran za'a yiwa kananan yara kimanin dubu 360 a yankunan kasashen da aka zaba wadanda suka fi samun yaduwar cutar ta Malaria.

Mary Hamed ta hukumar kula da ingancin magunguna ta tarayyar turai ta ce ana fata maganin zai rage kaifin tasirin kwayar cutar Plasmodium da ke haddasa cutar ta Malaria. Za a yiwa yara jarirai allurar sau uku cikin watanni biyar sannan a yi musu cikon na hudu lokacin da suka kai shekaru biyu da haihuwa. 

Cutar zazzabin cizon sauro na daga cikin cutattukan da ke hallaka kananan yara a wasu kasashe masu tasowa musamman na Afirka.