1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin Amerika a Afghanistan

August 16, 2010

Banbanci tsakanin gwamnatin Obama da sabon kwamandan ta a Afghanistan kan yaki da yan Taliban

https://p.dw.com/p/OovT
Janar David PetraeusHoto: AP

An samu sabanin ra'ayi tsakanin Sakataren tsaron Amurka da babban kwamandanta na Afghanistan, dangane da batun alkwarin nan da shugaba Obama yayi na fara janye sojojin kasar daga Afghanistan a watan yulin badi.

Sakataren tsaron Amirka wato Robert Gates ya bayyana cewa gwamantin Obama za ta cika alƙawarinta na fara janye sojojin Amurka daga Afghanistan a watan yuli badi, sabanin kwamandan Yakin Afghanistan da gwamnatin Obama ta da nada makwannin 6 da suka gabata Janar David Petraeus da shi kuma ke cewa suna bukatar lokaci don cim ma nasarar abin da suka sanya a gaba.

Janar Petraeus wanda shi ke jagorantar dakarun hadin gwiwa na kungiyar NATO da Amurka ke jagoranta a yakin Afghanistan, ya shaidawa duniya cewa akwai alamun za su samu nasara a wannan yaki, sai dai suna bukatar a yi musu hakuri a kuma basu isasshen lokaci don kai wa ga samun wannan nasara.

Haka kuma janar din yayi gargadin cewa fara janye sojojin Amurka daga watan yulin badi kamar yadda shugaba Barack Obama yayi Alkawari a baya, tamkarar ba da kai ne ga kungiyar gwagwarmayar kasar ta Taliban da Amurka ta hambare gwamnatinta a shekara ta 2001, kuma wata dama ce a gare su ta ci gaba da cin karensu babu babbaka.

Wannan kalami na janar Petraeus a zahiri sun nuna cewa baya goyan bayan Manufar Gwamnatin Obama ta fara janye sojojin Amurka daga Afghanistan.

A tattaunawar da yayi da manema labarai, janar din ya ce shugaba Obama ya tura shi Afghanistan ne ba wai don ya tsara yadda za a janye sojoji ba, ya tura shi don tabbatar da ganin ana samun ci gaba tare da ba da shawara a kan matakan da suka da ce a dauka.

O-ton

"Mun zauna da Obama a ofishinsa in da ya shaida mini cewa abin da ya fi bukata daga gare ni shi ne shawara, mun kuma dauki matakai da abubuwan da ake bukata wajen daukar wannan matakai da zarar kuwa an samu wani sauyi daga ciki tabbas zan sanar masa."

Janar Petraeus, yace abin da ya fahimta daga bayanin da Obama yayi kan fara janye sojojin, shi ne wani mataki ne za a fara dauka daki daki , ba wai wani al'amari ne da za a yi shi a lokaci guda ba. Sannan ya kuma ce sanin kowa ne a wasu lokuta a kan samu sabanin ra'ayi, yana mai cewa

O-ton

" Obama shugabane na kasa mai cin gashin kanta dole ne mu fahimci hakan, a mafi yawan lokuta ana samun fahimta iri daya akan al'amura, sai dai a wasu lokutan kuma ana samun sabanin ra'ayi."

Ko dama can mutane da dama sun soki wannan wa'adi da Obama ya tsayar na fara janye sojojin Amurkan daga Afghanistan a tsakiyar shekara mai zuwa, wadanda ke ganin yin hakan alamu ne ga kungiyar Taliban da yanzu haka ke ikon kudanci kasar cewa su ci gaba da jira domin Amurkan ba zata dauwama tana yakin ba.

Wasu kuwa sukarsa suke akan kin janye sojojin tun tuni daga yakin da suke ganin Amurka da kawayenta sun kasa samun nasararsa, maimakon haka ma a kullum rayukan sojojinsu ne ke ta salwanta.

Rahotanni sun bayyana cewa yawan sojojin kasashen waje da aka kashe tun bayan fara yakin na Afghanistan shekaru 9 da suka gabata sun haura mutum 2,000, wanda 1,226 daga ciki sojojin Amurka ne, 331 na Birtaniya, 445 kuma na sauran kasashen da ke cikin kawancen sojojin.

Mawallafi: Halima Umar Sani

Edita: Umaru Aliyu