1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Kwanaki 100 na luguden wuta da farautar 'yan Hamas a Gaza

Abdoulaye Mamane Amadou
January 14, 2024

Hukumomin lafiya a yankin Falasdinawa, sun bayyana mutuwar mutane fiye da dubu 23 tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da farmaki kan mayakan kungiyar Hamas

https://p.dw.com/p/4bDYV
Kwanaki na gwabza yaki tsakanin Isra'ila da mayakan Hamas
Kwanaki na gwabza yaki tsakanin Isra'ila da mayakan HamasHoto: Mohammed Dahman/AP Photo/picture alliance

Isra'ila ta ce ba wani abinda zai hanata ci gaba da kare manufofinta na kakkabe mayakan kungiyar Hamas daga Zirin Gaza, a yayin da yakin da ake gwabzawa tsakanin kasar da Hamas ya cika kwanaki 100.

A cikin wani taron manema labarai a birnin Tel-Aviv,  Firaminista Benjamin Netanyahu, ya ce ba wanda zai iya dakatar da manufofin da Isra'ila ta sa gaba na kawar da barazanar da take fuskanta daga Zirin Gaza.

Karin Bayani :  Antony Blinken ya yi tozali da Mahmud Abbas kan rikicin Hamas da Isra'ila

Wasu iyalan Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su, sun yi zanga-zangar nuna rashin jin dadi kan garkuwa da danginsu da ake ci gaba da yi, a yayin da wasu dumbin magoya bayan a dakatar da yakin da Isra'ila ke yi da Hamas, suka yi zanga-zangar neman a tsagaita buda wuta don shigar da kayayakin agaji a Gaza.

Karin Bayani : Isra'ila za ta bayyana a gaban kotun kasa da kasa

Luguden wutar da Isra'ila a sassan Gaza, a kokarinta na kakkabe mayakan Hamas da wasu manyan kasashe suka ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda, ya kashe Falasdinawa fiye da dubu 23 a cewar ma'aikatar lafiyar yankin Falasdinu.