1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin farfaganda a Iraki

December 4, 2005
https://p.dw.com/p/BvI7
A karon farko rundunar sojin Amirka a Iraqi ta amsa cewa ta ba wa kamfanonin buga jaridu na Iraqi toshiyar baki don buga labarai masu dadin ji game da aikin sojin Amirka kasar. Jaridar Washington Post ta rawaito wata sanarwa da ke cewa wannan lada bangare ne na wani halattacen kamfen da ake yi don hana buga bayyanai na karya game da ainihin abubuwan da masu ta da kayar baya ke yi. Da farko kafofin yada labarun Amirka sun ce ma´aikatar tsaron Amirka ta ba wa wani kamfanin kwangila tsara irin rahotannin da za´a rika bugawa a cikin jaridun Iraqi. Wadannan rahotannin kuwa dole ne su dace da ra´ayin sojojin Amirka a Iraqi. A wasu lokutan ma ana ba ´yan jaridar Iraqi makudan kudade don buga irin wadannan rahotanni.