1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

YaKin neman zaɓe a Russia

September 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuCI

A ƙasar Russia an buda yaƙin neman zaɓen yan majalisun dokoki, wanda zai wakana ranar 2 ga watan desember na wannan shekara.

Majalisar Douma ta ƙunshi yan majalisu 450, wanda jama´a fiye da milion 107, za su zaɓa a wannan rana.

Zaɓen na matsayin zakaran gwajin dafi ga zaɓen shugaban ƙasa na ranar 2 ga watan maris na shekara mai zuwa.

Masu kulla da harakokin siyasa a ƙasar Russia, na hasashen cewar babu ja, jam´iyar haɗin kan Russie, zata lashe zaɓen da gagaramin rinjaye.

A nasu ɓangare jam´iyun adawa, tunni, sun fara ƙorafe-ƙorafe, tare da zargin gwamnati da nuna masu rashin adalaci, wajen yin anfani da kafofin sadarwa na ƙasa.

Akwai alamun yan adawar ba za su taka rawar a zo a gani ba, ta la´akari da rarabuwar kanun da ta kunno kai tsakanin su.