1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin neman zabe a Amurka

Mansour bala BelloOctober 11, 2004

Yan takarar neman shugabancin Kasar Amurka na dada zafafa a tsakanin shugaba Bush da Senator John Kerry

https://p.dw.com/p/Bvfl
Senata Kerry da shugaba Bush
Senata Kerry da shugaba BushHoto: AP

Yakin neman zabe a can kAsar amurka na cigaba da zafafa a yayin da zaben kasar ke karatowa .A ranar alhamis mai zuwa ne zaa gudanar da mahawarar karshe a tsakanin yan takarar biyu domin nuna basirar da alla ya basu na kwazon su a fagen siyasar kasar tare da neman goyan bayan yan kasar a zaben na ranar 2 ga watan gobe idan Allah ya kaimu ..A yanzu haka dai shugaba Bush ya nufi jihohin Iowa Minnesota da kuma Missouri a yayin da senator John Kerry ya nufi Ohio da Florida .To sai dai wata majiya na cewa duka yan takarar basa cikin hayyacinsu a yayin da lamarin siyasar kasar na neman ya kasance Mace da Ciki wai abun da hausawa kance baa san abun da zata haifa ba A cigaba da kare matakin daya dauka na kifar da gwamnatin sadam Hussain shugaba bush ya soki John Kerry da kasancewa mai sauya kamanni a dangane da siyasar kasar da kuma batin yaki da iraq .Yace a cewar Kerry babu dalilin da zaisa a kifar da sadam daga madafan ikon kasar wanda kuma a hannu guda ya amince da yakin da kasar ta shiga da iraq a shekarar bara ..Shi kuwa a mayar da m,artani Kerry yace har kawo yanzu babu wata alama dake nuinni da cewa sadam nada makaman kare dangi da ake zarginsa da kerawa wanda shine makasudin yaki da iraq a baya .Kerry yace dole ne a dauki mataki daya cewa Bush ya tafka kuskure a dangane da bayanan karya daya yaudari yan kasar domin amincewa da yaki da iraq .Bugu da kari kerry ya bayyana cewa shekaru sama da 70 da suka shude baa sami gwamnatin data haifar da rashin aikinyi ba kamar ta Bush .,A jawabinsa ga yan kasar ta gidan rediyo Bush yace idan har Amerikawa sukai kuzskuran zabar Kerry ya zama shugaba to babu shakka kasar zata fuskanci barazana ta fannin tsaron da baa taba tsammani ba .Daya daga cikin mai bawa John Kerry shawara yace a yanzu haka yaki ne a tsakanin taklakawan Amerika da masu kudi a yayin da Bush ke bin bayan masu kudi Kerry na bin bayan talakawan kasar ne baki daya Yace idan har an tabo batuin fannin tattalin arzikin kasa da kiwon lafiya da kare muhalli to babu shakjka Kerry ya fita zakka .Tuni dai Bush yace idan da ace Kerry zai kasance shugaban Kasar Amurka a halin yanzu da Sadam Hussain ya kasance a kann karagar mulkin kasar iraq .To sai dai Kerry ya musanta hakan da cewa babu tabbas .Senator Kerry dan takarar jamiyyar demokrats a mahawarar farko shine kann gaba da bush bugu da kari shine kann gaba a mahawarar ta biyu ga Bush a cewar yawancin yan kasar da suka kalli mahawarar ta tashar kafafan yada labarun Kasar .har yanzu dai baa san maci tuwo ba abun da hausawa kance wai sai miya ta kare .