1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin neman zabe a Iran

Zainab A MohammadJune 1, 2005

Neman goyon bayan matasa

https://p.dw.com/p/BvbY
Hoto: AP

Ayayinda ake cigaba da kada kugen siyasa a kasar Iran,yan takaran kujeran shugabancin kasar na muradin yin nasara wajen samun kuriun matasa.

Yan takaran kujeran shugabanci a kasar Iran sun lashi takobin jan hankalin matasa wajen kada kuriunsu ,tare dayi musu alkawarin rage tsoma bakin yansandan addini cikin harkokin rayuwansu na yau da kullum,tare da inganta musu harkokin rayuwa da aladu da samar musu ayyukanyi,sabanin halin da suke ciki yanzu.

Ana dai ganin cewa kuriun matasan sune zasufiyin tasiri a zaben shugaban kasar ta Iran da zai gudana ranar 17 ga wannan wata,saboda sune mafi yawan alumman kasar matasa ne wadanda shekarunsu basu shige 25 ba,kuma shekarun kada kuria ya kama daga 15 a kasar ta Iran.

A zaben daya gudana a shekarun 1997 da 2001dai matasa sun taka rawar gani wajen kada kuriunsu,inda suka zabi Mohammad Khatami ,wanda keda daman tsawa takara har sau uku amatsayin shugaba a Iran.

To sai dai mutane da dama sun soki gwamnatinsa musamman dangane da gazawansa wajen yiwa dokokin addinin musulunci gyaran fuska,da sauya akidojin Iran a fuskar siyasa daga saniyar ware da kasashen yammaci suka mayar da ita,da kuma huldodi tsakanin maza da mata,kana da uwa uba matsalolin tattalin arzikin wannan kasa.

Domin neman goyon bayansu,tuni sauran yan takara 8 sukayi amfani da wadannan akidoji wajen shawo kann matasan su mara musu baya a wannan zabe mai zuwa.

Fitaccen dan takara Akbar Hashemi Rafsanjani,yace matasa nada muhimmiyar rawa da zasu taka a siyasar kowace kasa,domin hakane yake da matukar muhimmanci a basu yancin walwala wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Shi kuwa tsohon kakakin majalisa kuma dan takara Mehdi Karroubi yayi alkawarin kare yancin alummar kasar,inda raayinsu yazo daya da Mohsen Rezaie.

Yanzu haka dai kowane dan takara na kokarin ganin cewa ya samu karbuwa daga matasan kasar.a sassa daban daban na Tehran dai ana cigaba da gudanar da campaign na neman zabe,kuma bisa dukkan alamu matasan na shirin fadawa cikin siyasar kasar gadan gadan.

A wani sabon kurian neman raayin jamaa daya gudana yaua a kasar ta Iran,Dan takara Rafsanjani ne ke jagoranta da kashi 38 da digo 8 daga cikin dari na magoya baya.To sai dai hakan inji manazarta na nuni dacewa har yanzu da sauran rina aka wajen cimma kashi 50 daga cikin dari da ake bukata,domin gudun sake tafiye zagaye na biyu da babban abokin adawarsa.