1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin neman zabe a Jamhuriya Benin

Yahouza SadissouFebruary 17, 2006

A Jamhuriya Benin Jam´iyun siyasa sun shiga yakin neman zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/Bu1d

A Jamhuriya Benin, yau ne jam´iyun siyasa, su ka fara yaki neman zaben, shugaban kasa, da za ayi ranar 5 ga wata mai kamawa.

A baki daya, yan takara 26 ne, da su ka hito daga jam´iyu daban daban na kasa, su ka shiga gwagwarmar neman dare kujera shugabancin Jamhuriya Benin,, domin cenji shugaba mai ci yanzu Mathieu Kereku, dan shekarau 72 a dunia, wanda a wannan karo, ba shiga takara ba.

Shima, tsofan shugaban kasa, Nicephore Soglo, babban abokin adawar Kereku, ba shi cikin jerin yan takara.

Dukkan su 2, dokar kasa ta haramta masu shiga takara, dalili da yawan shekaru.

Saidai,tun ba a je ko ina ba, jami´un siyasa ,sun fara bayana rudani da zullumi, a game da yadda shirye shiryen zaben ke wakana.

Tun tsakiyar watan November a ka fara fuskantar matsalolin kudaden bayan da ministan kudi ya bayyana cewar, ba shi da issasun kudade shirya zaben,wanda yawan su ya tashi CFA billiard kussan 38 ,wato kimanin EUro million 49..

Sai a karshen watan Janairu, da ya gabata, bisa matsin lambar kasashen ketare da na kungiyoyin cikin gida, gwamanti ta matso CFA billiard daya da rabi ,daga cikin billiard 10 da da ake jira ta bada.

Sannan kungiyoyin kasa da kasa, su ka taimaka da biliar 4 da rabi.

Wannan jinkiri, da aka samu wajen tattara kudaden tafiyar da tsarin zaben, ya sa shirye shiryen baki daya na tafiyar haiwainiya.

Kasashe masu da hannu da shuni, da su ka hada da France da kungiyar gamayya turai, sun bayyana damuwa, game da jinkirin da a ke ci gaba da samu, ta fannin samar da kudaden shirya zaben.

A nasa bangaren shugaban hukumar zabe mai zama kanta Sylvain Nouwatin, ya tabatar da cewa, babu kwankawanto za ayi wannan zabe ranar 5 ga watan Maris ,sannan ya yi kira ga yan siyasa, da su kwantar da hankulla, su kuma gudanar da yakin neman zabe, cikin ladabi da fahintar juna.

Shugaban kasa Mathieu Kereku, ya ja hankullan membobin hukumar zabe mai kanta, da su yi anfani da kudaden da su ka samu, ta hanyar da ya dace.

Baki daya, mutane kimanin milion 4 ne, ya cencenta su kada kuri´u ranar zaben.

Saidai, ya zuwa yanzu, tunni wasu daga cikin yan takara, sun fara korafin shirya magudi.

Daya daga cikin su, Severin Adjovi, ya bayana cewa an samu kari ,na a kalla kashi 8 bisa 100, na yawan mutanen da ya cencenta su jefa kuri´a, a jihohin wasu daga membobin gwamnati.

Ranar 3 ga wata Maris za a kammala yakin neman zaben.

A wata sabuwa kuma, shugaba Mathieu Kereku, ya tsige ministan harakokin wajen kasar, Rogatien Biaou, bayan an tuhumi shi, da saida filaye mallakar Benin ,da ke kewaye, da opishin jikadancin kasar, a birnin Washington na Amurika.

Gwammnatin ta girka komitin bincike, domin gano gaskiyar al´ amarin.