1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yamutsi A Zirin Gaza

July 20, 2004

Ana fama da yamutsi da rashin sanin tabbas a zirin Gaza duk kuwa da janyewar da shugaban Palasdinawa malam Yassir Arafat yayi daga shawarar nadin dan-uwansa domin shugabancin hukumar tsaro ta yankunan dake da ikon cin gashin kansu

https://p.dw.com/p/Bvhx
Yamutsi da rashin sanin tabbas a zirin Gaza
Yamutsi da rashin sanin tabbas a zirin GazaHoto: AP

Bisa ga dukkan alamu dai hargitsin na baya-bayan nan yana mai yin nuni ne da wani yanayi na gwagwarmayar kama madafun iko da aka shiga a tsakanin Palasdinawa. Kafofin yada labaran Isra’ila ba su yi wata-wata ba wajen gabatar da rahotannin shiga wani hali na yamutsi da rashin sanin tabbas da kuma barazanar tarwatsewar kungiyar Fatah ta shugaban Palasdinawa Yassir Arafat. Shi kansa P/M Palasdinawan, mai ci Ahmad Qurei’i, sai da aka ji irin wannan bayanin daga bakinsa, ya kuma kara da cewar:

Tuni na mika wa Yassir Arafat takarda ta ta murabus. Babban dalili kuwa shi ne hali na yamutsin da aka shiga da kuma gazawar da aka yi wajen biya wa jama’a bukatunsu.

Ba kuwa Qurei’i kadai ba akwai jami’an siyasar Palasdinawa da dama dake sukan lamirin manufofin malam Yassir Arafat. Ga alamu gwagwarmayar kama madafun mulki ta dauki wani sabon salo a tsakanin Palasdinawan yanzu haka, a cewar Hisham Abdallah, manazarcin al’amuran siyasa, wanda ya ci gaba da bayani yana mai cewar:

An samu rarrabuwa tsakanin kungiyar Fatah zuwa wasu rukunoni guda biyu dake kalubalantar juna. A bangare guda akwai magoya bayan Yassir Arafat, wadanda ke ko oho da matsin lamba daga Amurka da Isra’ila domin aiwatar da garambawul a fannonin kudi da na siyasa, ko da yake ba sa kyamar ci gaba da shawarwarin sulhu da Isra’ila. Sannan a daya bangaren kuma akwai wani rukunin, wanda ya kunshi da yawa daga cikin shuagabannin Palasdinawan, amma baya da wani tasiri na a zo a gani. Wannan rukuni na goyan baya duk wata damar da ta samu ta shiga shawarwarin sulhu, hatta shawarar Isra’ila ta janyewa daga zirin Gaza ba tare da tuntubar Palasdinawa ba. Kazalika wannan rukuni na neman ganin an dauki safifan matakai na garambawul ga mahukuntan Palasdinawa, musamman ma hukumar tsaro.

Wannan rukuni ya hada har da Muhammed Dahlan, tsofon shugaban hukumar tsaro, wanda ke da kakkarfan tasiri a zirin Gaza. Wasu manazartan sun hakikan ce cewar wannan hali na yamutsi da aka shiga wani shiri ne da aka tsara tun da farkon fari, amma ba wata manufa ce ta ba wa kowa-da-kowa wata dama ta cin karensa babu babbaka ba. A dai wannan marra da ake ciki yanzu ba wanda ya san tahakikanin alkiblar da shi kansa P/M Palasdinawa Ahmad Qurei’i ya fuskanta, musamman ma ganin yadda ake zarginsa da laifin sayarwa da Isra’ila siminti, wanda kasar take amfani da wani bangare daga cikinsa wajen gina shigen da ake fama da sabani kansa yanzu haka. Abin da ake fargaba shi ne ka da a wayi gari gwamnatin Palasdinawan ta wargaje baki daya.