1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa a Gabon sun yi gangami

Abdourahamane HassaneSeptember 10, 2016

Dubban jama'a magoya bayan 'yan adawa a Gabon sun gudanar da wani gangami tare da yin marchi domin nuna alhini ga jama'ar da suka rasa rayukansu.

https://p.dw.com/p/1JzuG
Gabun Libreville Ausschreitungen nach Wahlen
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

A sakamakon tashin hankali da ya faru biyo bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da hukumar zabe ta yi a makon jiya wanda Ali Omar Bango ya lashe.
Jagoran 'yan adawar Jean Ping wanda ya jagoranci marchi tare da rakiyyar wasu 'yan adawar,ya jawabi a gaban wani dandali da aka yi marchin domin tunawa da wadanda suka mutu.Mutane akalla guda biyar suka rasa rayukansu a kasar ta Gabon a sakamakon tashin hankalin da ya barke bayan zaben shugaban kasar yayin da wasu da dama suka jikkata.