1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya:"Kwanaki 100 ya kamata a ga sauyi"

Uwais Abubakar Idris/YB September 4, 2015

Jam'iyyun adawar a Najeriyar sun ce akwai bukatar a tuna wa shugaba Buhari abin da ya alkawarta yi cikin kwanaki 100.

https://p.dw.com/p/1GROr
Niger Buhari Issoufou
Shugaba BuhariHoto: DW/M. Kanta

Fitowa karara a fili da fadar shugaban Najeriyar ta Aso Rock bisa cewa shugaba Buhari fa bai yi wa ‘yan Najeriyar wasu alkawura na abubuwan da zai yi a cikin kwanaki 100 da darewa kan karagar mulki ba ya sanya jam'iyyun adawar cewa akwai bukatar a tuna mashi abin da ya alkawarta yi, domin su da aka yi wa alkawari basu manta ba. Alhaji Abdulqadir Abdulsalami shi ne shugaban jamiyyar adawa ta Labour.

"Buhari da jamiyyar APC kuwa ai sun yi wa mutane alkawari, sun ce da sun zo lokaci Naira za ta koma dai dai da Dala, kuma a tsakanin lokaci kaza zuwa kaza Boko Haram zai zama tarihi, domin ko da matasa da aka ce za'a basu aiki ba'a ba wa kowa ba. Don haka a kwanaki 100 na mulkin nan bamu ga wani canji ba".

Ko da yake ga wadanda suka sa ran ganin an gudanar da irin bukuwan da aka saba yi a lokutan baya na cikar gwamnati kwanaki 100 a karagar mulki na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na cikin yanayi na murna to ko me ake ciki, ga tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma jigo a jamiyyar APC mai mulki Sanata Abdullahi Adamu ya ce ga duk wanda yasan makama ta mulki babu dalilin ma daga 'yar yatsa a kan wannan batu.

Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari
Shugaba Buhari bayan kama aikiHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba
Nigeria Präsident Goodluck Jonathan und Muhammadu Buhari
Kwanaki 100 da mika wa shugaba Buhari mulki daga tsohon shugaba JonathanHoto: Reuters/Afolabi Sotunde

"Abubuwan da gwamnatin Muhammadu Buhari ta shinfida a 'yan kwanakin nan sun fi karfin a ce an gina gada kaza ko asibi kaza, domin abuwan da ya sa gaba daga lokacin da aka nada shi zuwa yanzu su ne rayuwarmu ta dogara a kansu. Duk wanda ya san halin da muke ciki kafin hawa shugaba Buhari mulki ya san cewa kasar nan ta tabarbare, har ma sai ka ce wai shin akwai gwamnati kuwa. Wannan shi ne aikin da yafi kowane aiki na gwamnati wahala".

Ga jamiyyun adawa da ke koken cewa basu ga wani canji ba a kwanki 100 na shugaba Buhari ko da nade-naden da ya yi basu tsira daga irin sukar da suke yi ba, to sai dai Santa Danjuma Goje shugaban ‘yan majalisu na shiyar Arewa maso Gabas ya ce akwai abin da ya kamata fa a yi la'akari da shi.

Ya ce "Shugaba Buhari ya yi dai dai a ko'ina, ba ma a Najeriya ba duk duniya kamar yadda Barack Obama na Amirka ya shedar, wadanda ya baiwa mukamai a farko 'yan ajinsu ne ba wai ma 'yan garinsu ba. Kowane shugaban kasa yana da izinin ya zabi wadanda ya ga sun cancanta don ya basu aiki da zasu yi mashi bisa kwarewa. To in haka ne kuwa ya kamata a bashi dama ya zabi mutanen da yake so. Don haka abin da ya yi dai dai ne"

A yayin da ake ci gaba da cece-kuce a kan abin da gwamnatin ta cimma a kwanaki 100, al'ummar Najeriya na ci gaba da zura idanun ganin sauyin da suke kishirwar gani da zai canza rayuwarsu don raba su da talauci da matsalar rashin tsaro da suka fi adabarsu.