1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan adawa a Nepal sunyi watsi da tayin da sarki Gyanendra yayi musu

April 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv21

Babban dan adawa na kasar Nepal yayi fatali da tayin da sarki Gyanendra yayi na gudanar da babban zabe da kuma tattaunawar zaman lafiya,a kokarinsa na kwantar da adawa da ake yi da mulkinsa.

Shugaban jamiyar Nepali Congress,Girija Prasad Koirala,ya fadawa kanfanin dillancin labaru na Reuters cewa,sarkin bai tabo matasalar kasar ba.

Shugaban adawan ya fadi haka ne jim kadan bayan sarki Gyanendra cikin sakonsa na sabuwara shekarar addinin Hindu,ya sake jaddadda aniyarsa ta gudanar da zabe a kasar,kodayake bai saka ranar zaben ba.