1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa sun amince da gwamnati

Zainab Mohammed AbubakarApril 21, 2016

A Janhuriyar Nijar al'umma na ci-gaba da martani dangane da matakin da gamayyar 'yan adawa ta COPA ta dauka na umurtan 'yan majalisarta da su koma mukamansu.

https://p.dw.com/p/1IZgm
Niger Niamey Opposition
Hoto: DW/M. Kanta

Tun da farko dai kawancen 'yan adawan na COPA ta sanar da janye dukkan 'yan majalisarat daga cikin sabuwar gwamnatin kasar da aka kafa, bisa zargin bata bisa tsari.

Sai sanarwar data fito daga gamayyar kawancen tun a farkon wannan makon ya janyo martani daga bangarori daban daban na kasar musamman daga 'yan siyasa da masu lura da abun da ka je su zo.

A yayin da wasu ke yabawa wannan mataki a matsayin ci gaba ne a fannin hadin kan kasa da demokradiyya, wasu na ganin cewar 'yan adawan sun yi amai sun lashe, saboda zargin da suka yi na tafka magudi a zabubbukan kasar da aka gudanar a cikin watan maris da ya gabata