1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa sun juya baya ga majalisa a Togo

Salissou Boukari
September 15, 2017

'Yan majalisar dokoki na bangaren adawa a kasar Togo sun fice daga majalisar dokokin kasar, inda suka ce ayar dokar da gwamnati ta ke kan batun kawo sauye-sauye a kudin tsarin mulki bai tabo kayyade wa'adin mulki ba.

https://p.dw.com/p/2k45c
Proteste in Togo gegen Gnassingbe ARCHIV
Hoto: picture alliance/AA/ Alphonse Ken Logo

Ana iya cewa kasar Togo ta kasance ta sha bambam da sauran kasashe idan aka dubi irin karba-karba ta mulki da aka samu a wasu kasashen na Yammacin Afirka. Domin kuwa dukannin kasashen Yammacin Afirka sun saka batun kayyade wa'adin mulki na shugaban kasa da kuma batun gudanar da zaben zagaye na daya da na biyu a cikin kundin tsarin mulkinsu.

Shi dai batun kayyade wa'adin mulki batu ne mai muhimmanci da ya kasance a cikin tsarin Afirka na harkokin demokaradiyya da harkokin zabe da tafiyar da mulki na kungiyar ECOWAS wadda shugaban na Togo yake a matsayin jagoranta tun daga watan Yuni na wannan shekara. To ko me ya sa kasar ta Togo ta bambamta da sauran dangi kan wannan batu na demokaradiyya? Farfesa Victor Prudent Topanou malamin koyar da fannin shari'a ne a jami'ar Abomey-Calavi ta kasar Benin ya yi kokarin kawo wannan amsa.

"To nan ana iya tunawa da yadda mulkin dan kama karya marigayi Gnassingbe Eyademaya gudana, wanda kuma dansa ya gaje shi, domin mulkin ya bashi damar samun rundunar sojojin kasar ta bangarensa inda kashi 99 cikin 100 na manyan sojojin kasar duk sun fito ne daga kabila guda da kuma jiha guda. Kuma an matse duk wani dandali na nemen 'yanci."

Faure Gnassingbe, Präsident Togo
Hoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Cikin wata sanarwa, shugaban hukumar gudanarwa ta kungiyar ECOWAS Marcel Alain de Souza, ya yi kira ga bangarorin kasar ta Togo da su aiwatar da sauye-sauyen da ya kamata a kundin tsarin mulkin kasar, ta yadda za a iya kayyade wa'adin mulkin shugaban kasa ga wa'adi biyu kawai.

Bayan da 'yan adawa suka matsa kaimi kan gwamnatin ta Faure Gnassingbe, a halin yanzu gwamntin ta amince ta saka batun wadannan sauye-sauye a cikin kundin tsarin mulkin amma da sharadin cewa dokar ba za ta shafi mulkin da shugaban ya yi a baya ba, batun da 'yan adawan suka ce sam ba za ta sabu ba. Shugaban na Togo dai ya gaji kujerar mahaifinsa Eyadema wanda ya rasu a ranar biyar ga watan Febrairu na 2005 bayan da ya shafe shekaru 38 a mulki. Faure Gnassingbe ya gaji mahaifinsa daga ranar 24 ga watan Afrilu na 2005 sannan ya shirya zabukan da ya lashe a shekara ta 2010, da  2015 zaben da 'yan adawar kasar suka ce sam basu yarda da shi ba.