1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawan Nijar sun amince da jadawalin zabe

Abdoulaye Mamane Amadou/ MABNovember 26, 2015

Duk da bayar da kai da suka yi kan ranar da ya kamata a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa, amma kuma 'yan adawan Nijar sun bukaci da a kafa kwamiti don duba sarkakiyar da ke tattare da tsarin zabe.

https://p.dw.com/p/1HDBZ
Niger Anschlag auf Hama Amadou Opposition
Hoto: Mahaman Kanta

'Yan adawan Nijar sun amince da jadawalin zabe


Rana guda bangarorin siyasar Nijar suka shafe suna tattaunawa a kan batutuwan rejistar masu kada kuri'a da aikin hukumar zabe mai zaman kanta kafin 'yan adawa su amince da jadawalin zaben da zai gudana a 2016. A baya dai sun yi burus da duk ranukan da aka tsaida don gudanar da zaben na shugaba kasa da na 'yan majalisa.

Injiniya Rabilou Alhadji Kane kakakin jamiyyar MNSD Nassara mai adawa ya ce sun sassauto ne " ba wai wani tsoronsu muke ba ko sunfi karfinmu ba ko karfin soja ba aa. Amma muna son kasar ne saboda haka za mu tafi zabe."

An dai shafe tsawon watanni ana kai ruwa rana dangane da ranakun zaben da ma rashin wakilcin adawa a cikin hukumar zabe mai zaman kanta. 'Yan adawan Nijar suka ce daga cikin mutune 20 da ke jagorancinta, wakilai biyu zuwa uku suke da su. Sai dai taron majalisar ya amince da sake baiwa 'yan adawa damar shiga manya da kananan kwamitoci na hukumar ta zabe domin kawo karshen tankiyar siyasar da aka yi fama da ita.

Seini Oumarou Vorsitzender der Partei MNSD im Niger Afrika
Madugu 'yan adawan Nijar Seini Oumarou ya yi na'am da jadawalin zabeHoto: MNSD

A lokacin da DW Hausa ta tambayi Injiniya Rabilou Kane ko wannan mataki zai kawo karshen dambarwar siyasar Nijar? Sai ya ce " mun kama hanyar warwareta idan suka ci gaba da ladabi da biyeyya ga abubuwan da muke so, su kuma suka yarda da abinda muka shigar. Sai a ci gaba da tattaunawa dama zauren saboda tattaunawa ne aka budeshi, don kowa ya samu damar fayyace abinda ke damunsa na siyasa ko demokaradiya."

A ranar 2 ga watan Disemba ne kwamitin da ke bibiyar kundin rijistar masu zabe zai sake zama na musamman kan batun. '
Yan adawan Nijar da masu rinjaye sun yarda da a shigar da takarda a gaban kotun tsarin mulki da kotun kolin kasar don jin matsayin doka kan waandin mambobin kwamitin.