1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawar Kenya sun ce mutane 100 sun mutu

August 12, 2017

Jam'iyyar adawa a kasar Kenya, ta ce mutane 100 ne suka mutu a rikicin bayan zaben kasar, a dai dai lokacin da 'yan sandan kasar ke musanta amfani da harsashin gaske a kan masu zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/2i7xW
Kenia Unruhen nach dem Wahlenergebnis
Hoto: Picture-Alliance/AP Photo/B. Inganga

Bayyana shugaba Uhuru Kenyatta na kasar a matsayin wanda ya lashe zaben ranar Talata dai ba ta yi wa bangaren adawar kasar dadi ba. Akwai ma wasu bayanan da ke nunin cewa an sami asarar rayuka a hargitsin na Kenya, jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben da yammacin ranar Juma'a.

Kungiyar kare hakkin bil adama a kasar ta ce tana da alkaluman mutane 24 da suka mutu, galibinsu a Nairobi babban birnin kasar. Bangarorin adawar da suka bayyana zaben da zama haramtacce sun dora alhakin kashe-kashen a kan jami'an 'yan sanda, wadanda suka ce suna aiki ne son ransu.