1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan Africa sun koka game da danniya da ake musu

ibrahim saniJuly 6, 2005

Taron kolin masu fafutikar newarwa Africa yanci yazo dai dai da taron Kolin kasashen G8, ko menene dalili

https://p.dw.com/p/Bvav
Hoto: AP

A dai dai lokacin da shugabannin kasashe na G8 ke gudanar da taron kolin su na wuni biyu a Scotland a dai dai lokacin ne kuma wasu masu fafutikar nemarwa Africa yancin ta ke nasu taron a can Garin Fana na kasar Mali na tsawon kwanaki hudu.

Babban makasudin wannan taro dai shine a nuna adawa da wannan taron na G8 a hannu daya kuma da kara tunatar dasu cewa batutuwan daya kamata su tattauna na fitar da nahiyar ta Africa daga kangin na talauci da fatara da alama suna kaurace tattaunasu.

Bugu da kari taron zai kuma dudduba matsalolin da kasashen nahiyar ta Africa ke fuskanta a hannu daya kuma da bada shawarwari na yadda za a shawo kann al,amarin.

A cewar shugaban kungiyyar AADB Barry Aminata Toure,taron zai kuma fito da matakai na kara nanatawa kasashen Africa hakkokin da suka rataya a kansu a hannu daya kuma da matakan da kasashen na G8 yakamata su dauka bisa kokarin da suke na fatattakar talauci da fatara daga nahiyar ta Africa.

Game kuwa da zabar Garin Fana a matsayin guri na gudanar da wannan taro, Toure ya fadawa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa an zabi garin na Fana ne don ganin cewa gari ne da ake noma auduga wacce ake fita da ita izuwa kasuwar ta ta kasa da kasa.

Toure yaci gaba da cewa don nuna rashin jin dadin su game da yadda akewa kayayyakin da Africa ta kai izuwa kasuwar cinikayya ta kasa da kasa musanmamma Audugu ya kara haifar da matakin zabar garin na Fana ganin cewa yana daya daga cikin garuruwa a Africa dake noma Auduga mai yawan gaske da ake kaiwa izuwa kasuwar cinikayya ta kasa da kasar.

Mr Toure ya kara da cewa a game da rashin adalci da akewa kayyakin da suka fito daga nahiyar Africa a kasuwar kasa da kasa, musanmamma Auduga ya haifar da nahiyar Africa asarar yuro miliyan 600 a tsawon shekaru biyar wato daga 1998 izuwa 2003.

A dai cikin tsawon kwanaki hudun da zaayi ana gudanar da taron, wakilan da suka halarce shi ana sa ran zasu mayar da hankali wajen musayar miyau don karawa juna sani game da batutuwa da dama da suke addabar nahiyar Africa ciki kuwa har da shirin nan na Mdd na kokarin kawar da fatara daga doron kasa.

Wasu daga cikin wadannan batutuwa sun hadar da batun ilimi da fatara da cututtuka iri daban daban dake addabar da yawa daga cikin kasashen Nahiyar.

Haka kuma mahalarta taron zasu sa ido suga irin wainar siyasar da taron na G8 zai Toya don sanin inda akas dosa da kuma matakan daya kamata su kara tattaunawa a kansu don ganin cewa nahiyar Africa ba ayi mata yar zagalin zagalin ba.